Ranar Ƙudus: Juma’ar ƙarshen watan Ramadan ce ranar ƙudus ta duniya

0
267
Ranar Ƙudus: Juma'ar ƙarshen watan Ramadan ce ranar ƙudus ta duniya

Ranar Ƙudus: Juma’ar ƙarshen watan Ramadan ce ranar ƙudus ta duniya

Daga Idris Umar,Zariya

Juma’ar ƙarshe a watan Ramadan ita ce ranar ƙudus ta Duniya. Wadda wasu musulmi ke nuna goyon bayan Falasɗinawa waɗanda ake zalunta dare da rana.

Ranar Kudus ta duniya rana ce wacce alummar musulmi da wadanda ma ba musulmi ba masu fafutukar neman yanci a fadin duniya ke ci gaba da raya wannan rana da ke nuna Jarumtaka da tsayin dakar alummar Palasdinu a gwgwarmayar da suka kwashe shekaru suna yi ta kalubalantar HKI da take zub da jininsu ba tare da wani tausayi ba.

Ranar Kudus ‘ Wacce akafi sani a hukumance da Ranar Kudus ta Duniya, wani tarone shekara-shekara dake nuna goyon bayan ga al’umma Falasdinawa da ake gudanarwa a ranar Juma’ar karshe na watan Ramadan don nuna goyon baya ga Falasdinawa da adawa da ƙasar Isra’ila da yahudawan sahayoniya. An fara gudanar da taron ne a shekarar 1979 a Iran jim kadan bayan juyin juya halin Musulunci.

KU KUMA KARANTA:Rundunar ‘yansanda ta hana hawan Sallah a Kano

Ana kuma gudanar da ranar Qudus a wasu kasashe da dama musamman a kasashen Larabawa da sauran kasashen musulmi, ciki harda Najeriya inda ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mamayar da Isra’ila ke yi a gabashin birnin Kudus. Ana gudanar da taruka a kasashe daban-daban na al’ummar musulmi da ma wadanda ba musulmi ba a duniya.

Masu sukar ranar Kudus suna jayayya cewa ana fakewa ne da ranar don kyamar Yahudawa. A Iran a ranar Kudus ana gabatar da zanga-zangar adawa da wasu kasashe, ciki har da Amurka da Saudiyya. Bincike ya nuna cewa a shekarar 1979, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ebrahim Yazdi ne ya fara ba da shawarar gudanar da zanga-zangar adawa da sahyoniyawa a kowace shekara ga jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ruhollah Khomeini. A lokacin, abin da ya fi daukar hankali yana da alaka da zurfafa takun saka tsakanin Isra’ila da Lebanon. Khumaini ya amince da ra’ayin Yazdi, kuma a ranar 7 ga watan Agustan 1979, ya ayyana ranar Juma’ar karshe ta kowane Ramadana a matsayin “Ranar Kudus”, inda musulmin duniya za su hada kai don nuna goyon baya ga Falasdinawa, dakuma nuna kyama ga mamayar Isra’ila kan Falasdinawa. Khumaini ya bayyana cewa ‘yantar da Kudus wani aiki ne na addini a kan dukkan musulmi:

Kadan daga cikin maganar khumaini

Ina kira ga al’ummar musulmi a fadin duniya da su tsarkake Juma’ar karshe ta watan Ramadan a matsayin ranar Kudus tare da shelanta hadin kan musulmi na duniya wajen goyon bayan halalcin hakkokin al’ummar musulmin Palastinu. Shekaru da dama ina sanar da al’ummar musulmi irin hadarin da ke tattare da haramtacciyar kasar Isra’ila wacce a yau ta zafafa hare-haren wuce gona da iri kan ‘yan’uwa Palasdinu, wanda a kudancin kasar Labanon ke ci gaba da kai hare-hare kan gidajen Falasdinawa.

Leave a Reply