Farfesa Adamu Ahmed ya zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello na 14

0
8
Farfesa Adamu Ahmed ya zama shugaban jami'ar Ahmadu Bello na 14

Farfesa Adamu Ahmed ya zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello na 14

Daga Idris Umar,Zariya.

Hukumar gudanarwar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta amince da nada Farfesa Ahmed Adamu a matsayin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na 14.

Bincike ya nuna cewa Farfesa Ahmed na ɗaya daga cikin mutane 14 masu neman matsayin wadanda kwamitin gudanarwar jami’ar wanda Alhaji Yayale ke shugabanta ya tantance.

Farfesa Adamu Ahmed ya kasance masani ne sosai a bangaren ilimi, inda ya ke da kwarewar aiki na sama da shekaru 30 a jami’ar Ahmadu Bello. Sananne ne har wa yau a bangaren ilimi da shugabanci, inda aka nada shi a matsayin mataimakin shugaban jami’ar ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Kano kuma shugaban hukumar gudanarwar jami’ar wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.

KU KUMA KARANTA:Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta yi bikin yaye ɗalibai kashi na 44

Nada Farfesa Ahmed Adamu a matsayin sabon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ana ganinsa a matsayin nadin da aka yi biyo bayan kasancewarsa sananne a bangaren ilimi da kuma salon shugabanci irin wanda ya ke da shi.

Jama’ar jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki sun zaku suna jiran rantsar da Farfesa Adamu Ahmed a hukumance a matsayin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na 14.

Leave a Reply