‘Yan bindiga a Yobe, sun kashe mutane 7, sun jikkata da dama
…Gwamnan Yobe, ya jajantawa waɗanda abin ya shafa
Daga Ibraheem El-Tafseer
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun kashe aƙalla mutane bakwai ‘yan kasuwa ne tare da raunata mutane 11, a kasuwar shanu da kuma babbar kasuwar Ngalda da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.
‘Yan bindigar da ake zargin, sun kai farmaki kasuwar mako-mako da ke Ngalda da misalin ƙarfe 6 na yamma suna harbe-harbe tare da yin fashin shaguna a tsakiyar kasuwar.
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙaramar hukumar Fika a dandalin sada zumunta, Dauda Yakubu Damazai, ya shaidawa manema labarai cewa wasu ‘yan kasuwa guda bakwai a babbar kasuwa da kasuwar shanu sun rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.
‘’A ranar Litinin da yamma wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a kasuwar shanu da babbar kasuwar Ngalda. Maharan sun kashe mutane bakwai da ba su ji ba ba su gani ba.
‘’Aƙalla mutane goma sha daya ne suka samu raunuka. An garzaya da su babban asibitin Fika domin jinya. Alhamdu lillahi jami’an tsaro da ‘yan banga sun kashe uku daga cikin maharan.
Gwamnatin jihar Yobe ta aike da wata babbar tawaga domin jajantawa iyalan waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka yi musu fashi da makami a Ngalda, ƙaramar hukumar Fika.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Ciroma Buba Mashio ne ya jagoranci tawagar tare da wasu manyan jami’an gwamnati da jami’an tsaro a matsayin mambobin tawagar.
Gwamna Buni ya jajantawa iyalan waɗanda aka kashe, ya kuma jajanta wa wadanda suka samu raunuka, da kuma ɗaukacin al’ummar Ngalda.
Ya kuma ba da umarnin a tallafa wa waɗanda abin ya shafa domin tallafa wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka samu raunuka.
KU KUMA KARANTA:An naɗa sabon shugaban Jami’ar jihar Yobe na riƙo
‘’Shugaban ƙaramar hukumar Fika, Hon Audu Bukar Gadaka, ya kai ziyarar jajantawa waɗanda lamarin ya shafa tare da yi musu addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma yi fatan samun sauƙi ga waɗanda ke kwance a asibiti.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce wasu gungun ‘yan fashi da makami ne su 6, ƙarƙashin jagorancin Datti Alhaji Dadji na garin Ngalda ne suka ƙaddamar da harin.
Ya ce lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai da jikkata goma sha ɗaya. ‘Yan fashin sun yi awon gaba da kimanin Naira miliyan 16.5.
‘’A martanin da suka mayar, mutanen garin Ngalda sun haɗa kai suka kashe uku daga cikin ‘yan fashin, yayin da wasu uku suka tsere da raunuka.
‘’Dan sanda DPO ya jagoranci tawagar ‘yan sintiri zuwa gidan Alhaji Dadji, inda suka ƙwato wata ƙaramar bindiga da aka ƙera a cikin gida ɗauke da harsashi uku. An kama Alhaji Dadji kuma a halin yanzu yana hannun ‘yansanda, inda yake fuskantar tambayoyi yayin da ake gudanar da bincike.
“An kwashe waɗanda abin ya shafa da gawarwakin zuwa babban asibitin Fika domin duba lafiyarsu da kuma tantance gawarwakinsu. Kwamishinan ‘yansanda, CP Garba Ahmed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin, ya kuma yi ƙira da a kwantar da hankula,”.