JOHESU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

0
35
JOHESU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

JOHESU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan jinya na Najeriya (JOHESU) ta ayyana shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, tun daga ranar Juma’a.

Yajin aikin baya-bayan nan na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da ƙungiyar ta baiwa gwamnatin Najeriya.

Yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja, shugaban JOHESU na ƙasa, Kabiru Minjibir, ya zayyana wasu daga cikin buƙatun nasu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar

Buƙatun sun haɗa da gaggauta aiwatar da dunƙulallen tsarin albashin ma’aikatan jinya da biyan ƙarin kaso 25 cikin 100 na basussukan da suke bin gwamnatin daga watan Yuni zuwa Disambar 2023 da ƙara shekarun ritayar ma’aikatan jinya da kuma yafe haraji a kan kuɗaɗen alawus ɗin ma’aikatan jinya da kuma gaggauta biyan bashin alawus ɗin shiga hatsari na lokacin annobar korona.

Ƙungiyar ta buƙaci dukkanin mambobinta dake faɗin Najeriya su yi biyayya ga wannan umarni.

Leave a Reply