Gwamnatin Amurka ta yi farin ciki da sakin jami’in Binance Gambaryan

0
76

Gwamnatin Amurka ta yi farin ciki da sakin jami’in Binance Gambaryan

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.

Gwamnatin Amurka ta bayyana farin cikinta da sakin babban jami’in kamfanin Binance Tigran Gambaryan da Najeriya ta yi.

Hakan na kunshe ne a sanarwar da mashawarcin shugaban Amurka a kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya fitar a yau Alhamis.

An ruwaito sanarwar na cewa, “ina mai farin cikin bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta saki ba-Amurke kuma tsohon jami’in tsaron Amurka Tigran Gambaryan a bisa dalilai na jin kai kuma yana kan hanyarsa ta komawa Amurka domin samun kulawar likitocin data dace.”

“Muna kamala tabbatar da sakin Mr. Gambaryan, na kira matarsa, Yuki, na shaida mata daddadan labarin.

KU KUMA KARANTA:An gurfanar da jami’in Binance a gaban kotun Najeriya

“Ina matukar godiya ga abokan aikina na najeriya wadanda tattaunawar da muka yi dasu tayi sanadiyar daukar wannan mataki kuma ina sa ran yin aiki tare dasu a fannoni da dama na kawance da hadin gwiwar kasa da kasa tsakanin kasashenmu 2” a cewarsa.

Gambaryan ya kasance a tsare ya na fuskantar shari’a a kan halasta kudaden haram tun cikin watan Afrilun da ya gabata.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.

Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ne ya sanar da janye tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba 23 ga watan Oktoba da muke ciki.

Leave a Reply