‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a Haiti

0
68
'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a Haiti

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 70 a Haiti

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bi sahun firai ministan ƙasar Haiti a ranar Juma’a wajen yin Allah wadai da wani mummunan harin da gungun ‘yan daba suka kai kan wani gari da ke wajen babban birnin ƙasar Haiti, wanda ya kashe aƙalla mutane 70, ciki har da mata aƙalla 10 da jarirai uku cikin dare.

Firai Ministan Garry Conille ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, “Za’a farauto waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya, ba tare da ɓata lokaci ba.”

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Haiti ta ce mambobin ƙungiyar Gran Grif ne suka kai harin a garin Pont Sonde da ke sashen Artibonite.

Wani rahoto da jaridar Haiti Gazette ta fitar ta ce ‘yan kungiyar na kokarin karbar kudi ne daga hannun al’ummar yankin kuma suka ki ba su. Kisan kiyashi zalunci ne.

Ofishihn kare hakkin bil adama na Malisar Dinkin Duniya ya ce mambobin kungiyar da ke harba bindigogi masu sarrafa kan su sun kuma kona gidaje akalla 45 da motoci 34, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankin tserewa.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

Harin dai ya raba akalla mutum 3,000 da muhallan su.

Mutane da dama sun samu rauni, ciki har da biyu daga mambobin ‘yan bindigar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum sha shida suna fama da mummunan rauni. Gwamnatin kasar ta ce an duba wadanda suka samu raunukan a asibitin gwamnati na Saint-Nicolas da ke Saint-Marc.

A watan Yunin da ya gabata, wata tawagar tallafawa tsaro ta kasa da kasa ko MSS, ta fara tura ‘yan sanda kusan 400 daga Kenya, wadda ita ce ke jagorantar aiki samar da zaman lafiya.

An tura wasu kimanin 100 daga Jamaica da Belize, don taimakawa ‘yan sandan kasar Haiti da ke fama da rikici wajen murkushe kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda ke addabar babban birnin kasar da kuma wasu yankuna da ke waje.

Ana sa rana sauran kasashe suma su aike da gudumuwar jami’an ‘yan sanda zuwa rundunar.

Leave a Reply