Ɗan sanda ya kashe wani mutum kan ₦200

0
30
Ɗan sanda ya kashe wani mutum kan ₦200

Ɗan sanda ya kashe wani mutum kan ₦200

Wani Insfektan ’yansanda ya caka wa mutum wuka har lahira kan cin hancin Naira 200 a garin Damaturu, fadar Jihar Yobe.

Ana zargin ɗan sandan da hallaka wani wanda ake zargin dillalin kwayoyi ne saboda ya ki ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema.

Lamarin ya faru ne a Unguwar CMC, Zango, Damaturu, inda sufeto Mohammed Bulama, da marigayin suka fafata ranar Lahadi da karfe 5:05 na yamma.

Wata majiya ta ce “Sufeto Mohammed Bulama ya bukaci N200 daga hannun mamacin.

KU KUMA KARANTA: Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu

“Da mamcin ya ki amincewa, sai Insifeto Bulama ya kai masa hari da wuka, inda ya yanke masa wuya da kirji har ya kai ga mutuwarsa.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yansandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce kwamishinan runduanr, Garba Ahmed ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Da yake ƙarin haske game da lamarin, jami’in ya ce takaddamar kan wani ciniki “ya rikiɗe zuwa faɗa, lamarin da ya sa Bulama ya daba wa Dauda wuka a kirji, shi ma Bulama ya samu rauni a kai.

“Ba tare da ɓata lokaci ba an kama wanda ake zargin a hedikwatar ’yansanda ta ‘C’ Dibision inda ya nemi mafaka.

“Sashen binciken manyan laifuka (CID) ta fara gudanar da bincike kuma a halin yanzu Bulama yana tsare a hannun har sai an gurfanar da shi a gaban kotu.” Inji shi.

Leave a Reply