Najeriya ta dasa bishiyoyi na tsawon kilomita 1500

0
91
Najeriya ta dasa bishiyoyi na tsawon kilomita 1500

Najeriya ta dasa bishiyoyi na tsawon kilomita 1500

Hukumar samar da shingen kare hamada ta ce aikin nan na dasa bishiyoyi tsawon kilomita 1500 a jihohi 11 na arewacin Najeriya domin yaƙi da hamada na samun nasara.

Shugaban hukumar Saleh Abubakar ya bayyana haka a bitar ayyukan hukumar, yayin da ɗumamar yanayi ke ƙara barazana ga ƙasashen da ke kudancin Sahel.

Gaba ɗaya jihohin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar na cikin wannan aiki wanda fadin sa kuma ta cikin kasa ya kai kilomita 50.

Babbar matsalar yanzu shi ne yanda wasu bata gari kan sace shingen kare bishiyoyin da ma bututun rijiyoyin burtsatse da ke shayar da bishiyoyin. “wadannan bishiyoyin su ke hana zafi ya gallabi jama’a, mu samu iskar OXYGEN ta wadata a yanayinmu; kowa ya san irin zafin da a ka shiga bana” Inji Abubakar Saleh.

KU KUMA KARANTA:Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Babban daratan ya ce ba za a iya hana mutane sare dukkan bishiyoyi don itacen girki ba, amma ya zama wajibi kowacce bishiya da a ka sare a maida gurbin ta “in ba ka iya samun Gas don girki ba, saboda karfin mutane ba daya ba ne to akwai fasahar shuka bishiyoyi da za a samu guma-gumai da za a yi rumbun gawayi, wanda shi ma ba shi da illa ga yanayi”.

Darakta Abubakar ya yi albishir ga jama’a cewa duk wanda ya dasa bishiyoyi ya raine su za a rika biyan sa ladar hakan da dalar Amurka duk shekara daga tsarin nan na CARBON CREDIT, wanda kasashe masu masana’antu da ke gurbata yanayi ke samar da makudan kudi don samar da bishiyoyi da za su kare duniya daga hanyoyin da ke illa ga malafar nan ta duniya OZONE LAYER da ke ba da kariya daga zafin rana.

‘Yan Najeriya irin su malamin makaranta Imran Adam, yace ya kan yi amfani da Gas wajen girki don a birane “ice ko gawayi” ma na da wuyar samuwa ko ba ma muhallin amfani da su.

Hukumar shingen Hamadar ta ce za ta shiga aikin wayar da kai don duk jama’a su dasa akalla bishiya daya a rayuwar su don bada gudunmawa ga al’ummar da ke zuwa nan gaba.

Leave a Reply