Amurka ta zargi China Da yin harshen Damo a Yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine

0
41
Amurka ta zargi China Da yin harshen Damo a Yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine

Amurka ta zargi China Da yin harshen Damo a Yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine

Amurka da China na shirye-shiryen wata tattaunawa tsakanin shugaba Joe Biden da shugaba Xi Jinping cikin kwanaki masu zuwa, inda ake sa ran batun tallafin da China ke baiwa Rasha a yaƙin Ukraine zama cikin muhimman batutuwan dake jadawalin Amurka.

Blinken ya tattauna da takwaran shi na China Wang Yi a gefen babban taron MDD a birnin NY a Amurka.

A karshen tattaunawar ta sama da tsawon sa’a guda, Blinken ya shaidawa manema labarai, a yayin wani taron manema labarai cewa, dole ne duk wani shirin samar da zaman lafiya da Rasha ke da shin a kawo karshen yakin da Rasha keyi a Ukraine ya kasance bisa bisa tanaje tanajen tsarin MDD musamman mutunta kasa da tabbatar da yancin kai.

KU KUMA KARANTA:Iran ta tallafawa Rasha da makamai a yaƙi da Ukraine

Da aka tambaye shi game da kallon da yake ma kokarin samar da jarjrjrniyar zaman lafiya da China da Brazil keyi, Blinken yace, zaman lafiya a inda mai zalunnci ke samun duk abinda ya nema, shi kuma wanda ake zalunta bas hi da wata damar da zai rike, kwata kwata wannan ba turba ce ta zaman lafiya mai dorewa ba, wadda ba adalci a ciki.

Tun da farko a ranar Juma’a kasashen China da Brazil sun aza kaimi wajen tattaro goyon bayan kasashe masu tasowa domin mara baya ga kudurin na China kan kawo karshen Yakin Rasha a Ukraine, duk da watsi da hakan da shugaban Ukraine din Velodymyr Zelensky yayi, bisa yiwa kudurin kallon dan lele ga muradun Moscow.

Tattaunawar da aka yi tsakanin Blinken da Wang ta zo ne a dai dai lokacin da Amurka ke kara damuwa kan yadda kamfanonin China ke samar da na’urori da suka hada da jirage marasa matuki ga Moscow, lamarin da ya karfafa katabus din da Rasha ke da shi a fagen daga a yakin da ta keyi a Ukraine.

Leave a Reply