No menu items!

Sample Page Title

Date:

NAFDAC ta rufe wani kamfani a Legas mai samar da jabun kayan kwalliya

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta rufe wata haramtacciyar masana’anta da ke samar da jabun kayan kwalliya a rukunin shagunan Benue Plaza da ke Filin Bajekoli a jihar Legas.

NAFDAC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce an rufe masana’antar ne bayan da jami’anta suka kai samame tare da gano wasu sinadarai da kayayyakin da ba su da rajista, da kuma waɗanda lokacin amfani da su ya wuce suka lallace.

A yayin gudanar da aikin, hukumar ta NAFDAC ta kama fiye da kwali 1,200 na kayan kwalliya na jabu.

Kayayyakin sun haɗa da ƙananan mazubai na haɗe-haɗe, da sinadarai marasa tambari da ma wasu na’urori, inda aka ƙwace aka kai su ofishin NAFDAC domin ci gaba da bincike.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta dakatar da anfani da sabulun wanka na Dove

“Hukumar ta ƙiyasta darajar kayayyakin da aka ƙwace a farashin kan titi inda ya kai kusan naira miliyan 50,” in ji NAFDAC.

Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...