Mun tafka mummunar asara – ’Yan kasuwa

0
102
Mun tafka mummunar asara - ’Yan kasuwa

Mun tafka mummunar asara – ’Yan kasuwa

’Yan kasuwar Monday Market da sauransu a Maiduguri sun tafka mummunar asara sakamakon ambaliya bayan fashewar Madatsar Ruwa ta Alau mai nisan kilomita 10 daga garin.

Ranar Litinin da tsakar dare ambaliyar ta yunkuro, inda ta raba dubban mazauna unguwannin Post Office, Gwange, Moromoro, Gadar Customs, Gidan Zoo, Bulabullin, Maidoki  Roundabout, Jami’ar Maiduguri, Cocin Saint Patrick da sauaransu da muhallansu.

Wani ɗan kasuwa ya ce, “Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su.”

Wasu daga cikinsu sun nuna matukar kaɗuwarsu da kuma tunanin yiyuwar maye gurbin abin da suka rasa a ambaliyar.

Wani mai sayar da sukari da fulawa a kasuwar, Muhammad Bulama, ya ce ambaliyar ta shanye kasuwar gaba ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

“Duk shagunanmu da ke kallon gidan Marigayi Alhaji Mai Sugar sun yi ambaliya, sukari da fulawa da shinkafa da kayan girki na miliyoyin Naira sun lalace.

“A sa mu a add’ua! Buhunan kayan abinci irin su sukari da shinkafa da gishiri da taliya da sauransu duk sun jike sun narke,” in ji shi.

Wakilinmu ya lura yawan ruwan da ke ambaliyar yana ƙara karuwa inda yake ƙara shiga wasu unguwanni.

Hakazalika ambaliya ta mamaye Gidan Zoo na Kyarimi ta wuce da namun dajin da ke ciki, inda a halin da ake ciki namun dajin suke neman mafaka.

Wani mazaunin yankin ya ce, “yanzu haka mun fice daga unugwar saboda gudun hari daga namun daji da kwarin da ke gidan zoo.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Borno ta buƙaci jama’a da su ƙaurace wa yankunan da aka samu ambabaliya zuwa wasu wurare masu aminci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here