No menu items!

Sample Page Title

Date:

Al’ummar Gobir sun shiga zullumi bayan fitowar bidiyon basarakensu da aka sace

Iyalai da talakawan daular Gobir da ke Sakkwato na ci gaba da zaman zullumi saboda ɓullar wani faifan bidiyo na basaraken daular da ‘yan bindiga suka sace yau fiye da sati uku, su ke ci gaba da barazana ga rayuwarsa da ta ɗansa da aka sace su tare.

Kawo yanzu dai hukuma ko Masarautar Sarkin Musulmi ba su ce uffan ba, duk da faifan bidiyon da ke nuna basaraken yana dab da rasa ransa.

An dai sace basaraken ranar 27 ga Yuli 2024, yau mako uku da kwana biyu.

A faifan bidiyon, ana ganin basaraken ɗaure da sarka jini ya zuba a gaban tufan da yake saye da ita, basaraken ya yi bayani a kan uƙubar da yake sha hannu wadanda suka yi garkuwa da shi, tare da dansa, har ta kai ga an yi musu alkawalin kisa in ba a biya kuɗin fansarsu ba.

KU KUMA KARANTA: Basaraken da ake nema game da kisan sojoji ya miƙa kansa

Wannan bidiyon dai a cewar iyalansa ya tayar musu da hankali ganin har yanzu mahukunta ba su ɗau wani mataki ba wajen fitowarsa har yana dab da barin duniya.

Har iyau iyalan na sa sun nemi agaji daga jama’a don samun kuɓutar da mahaifin su.

A halin da ake ciki a garin Sabon Birni wannan faifan bidiyon ya tayar da hankulan talakawa a cewar wani mutumin garin Muhammad Abdullahi Gobir.

Kawo yanzu dai ba hukumar da ta fito a bayyane ta yi magana a kan basaraken duk da fitowar wannan faifan bidiyon, duk da yake Mataimakin Gwamanan jihar, Idris Muhammad Gobir, ɗan asalin Sabon Birni, basarakensu ne ke fuskantar barazanar mutuwa hannu ‘yan bindiga din.

Duk da yake gwamnan Sakkwato yana cewa gwamnatinsa na ƙoƙari wajen samar da tsaro, amma dai har yanzu mutanen Sabon Birni da wasu sassan gabashin Sakkwato suna cikin mummunan yanayi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...