Yadda zanga-zangar tsadar rayuwa ta koma tarzoma a Yobe
Daga Ibraheem El-Tafseer
Kamar sauran garuruwa a faɗin Najeriya, yau 1 ga watan Agusta, 2024 aka fara zanga-zangar tsadar rayuwa a wasu garuruwa na faɗin ƙasar.
A garin Potiskum da ke jihar Yobe ma an fita, an fara zanga-zangar ne da gangami a ƙofar Sinima da ke tsohuwar Kasuwa Potiskum. Matasan ɗauke da takardu masu nuna cewa “muna fama da yunwa, a dawo da tallafin man fetur”.
Sannan ɗaya daga cikin matasan ya yi ƙira ga shugaba Tinubu da ya gaggauta kawo mafita a ƙasar, saboda jama’a da dama suna mutuwa sakamakon yunwa da tsananin talauci da ake fama da shi a ƙasar.
Daga nan ne fa matasan suka fantsama kan tituna, inda kusan dukkan ɓangarorin garin babu inda matasan ba su fito ba.
KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga: Gwamnatin Yobe ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a Potiskum, Nguru da Gashuwa
Amma kash! A ƙarshe zanga-zangar ta koma tarzoma, inda suka fara ƙone-ƙonen tayoyi akan tituna, sannan suka rufe titunan da manyan duwatsu.
Matasan sun ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Potiskum da Ofishin Zaɓe (INEC), sannan sun je gidan Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu, Sanata Ibrahim Bomoi (Bala Basa) sun farfasa wani ɓangare na gidan, ba don zuwan jami’an tsaro ba, da sun ƙona gidan. Jami’an tsaro ne suka tarwatsa su da Tiyagas.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin jihar Yobe ta saka dokar taƙaita zirga-zirga a garin na Potiskum da garuruwan Gashuwa da Nguru.