Trump da Harris sun yi tir da zanga-zangar ƙin jinin Isra’ila

0
69
Trump da Harris sun yi tir da zanga-zangar ƙin jinin Isra'ila

Trump da Harris sun yi tir da zanga-zangar ƙin jinin Isra’ila

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ke ƙare yaƙin da ƙasar ke yi a Gaza, a yayin jawabi da ya yi a zauren Majalisar dokokin Amurka.

Manyan ‘yan takarar shugabancin Amurka biyu, mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da tsohon shugaban ƙasa Donald Trump, sun ya yi Allah-wadai da zanga-zangar nuna adawa da Isra’ila wacce aka fara ranar Laraba a kusa da ginin majalisar dokokin Amurka.

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ke kare yaƙin da ƙasar ke yi a Gaza, a yayin jawabi da ya yi a zauren Majalisar dokokin Amurka.

Harris, wacce ta yiwu ita ce ‘yar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar Democrat a zaɓen shekarar nan ta 2024, a cikin wata Sanarwa ta ce “Mun ga ayyukan Allah-wadai daga marasa kishin ƙasa masu zanga-zanga da munanan kalaman ƙiyayya a tashar jirgin ƙasa ta Union Station da ke kusa da ginin majalisar dokoki.”

KU KUMA KARANTA:Joe Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka

A gaban tashar, masu zanga-zangar sun cire tutocin Amurka suka sanya Tutocin Falasɗinawa, sannan wani mutum ya yi amfani da jan fenti ya rubuta “Hamas na nan tafe” da manyan harrufa a kan wani babban sassaƙe. Bayan haka Masu zanga-zangar sun ƙona wani mutum-mutumi na Netanyahu da tutar Amurka.

Shi ma Trump, ya rubuta a shafin sa na sada zumunta na Truth cewa “Idan da waɗanda suka ta da tarzoma jiya a Washington ‘yan Republican ne, da yanzu dukkansu na tsare a gidan yari, suna fuskantar hukuncin ɗauri na shekaru 10 zuwa 20. Amma a ƙarƙashin wannan Gwamnatin, babu abin da zai same su.”

A jiya Alhamis Shugaban Amurka Joe Biden ya karɓi baƙuncin Firai Minista Benjamin Netanyahu a fadar White House, don tattaunawa da nufin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin sauran mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, tun bayan harin da ta kai kan Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Shugabannin biyu sun gana a Ofishin shugaban kasa, kwana daya bayan da dukkansu sun gabatar da muhimman jawabai. A ranar Laraba Netanyahu ya yi magana a gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda ya kare yaƙin da ƙasarsa ke yi da mayaƙan Hamas.

Shi kuwa shugaba Biden ya yi jawabi game da dalilin da ya sa ya yanke shawarar janyewa daga takarar shugaban ƙasa a ranar Lahadin da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansa ga mataimakiyarsa.

 

Dukkan shugabannin biyu sun gabatar muhimman jawabai a taƙaice kafin ganawar da suka yi ta sirri.

To sai dai gabanin ganawar, wani babban jami’in gwamnatin ƙasar ya shaidawa manema labarai cewa shugabannin biyun suna aiki kan cikakkun bayanai game da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin waɗanda aka yi garkuwa da su, “wadda suka ce sun yi imani ana a matakin ƙarshe.”

Leave a Reply