Abin da ya sa ɗalibi ya fashe da kuka don ya faɗi a gasar ‘Spelling Bee’ a Yobe

0
63
Abin da ya sa ɗalibi ya fashe da kuka don ya faɗi a gasar 'Spelling Bee' a Yobe

Abin da ya sa ɗalibi ya fashe da kuka don ya faɗi a gasar ‘Spelling Bee’ a Yobe

Ɗaya daga cikin ɗaliban da suka yi matuƙar ƙoƙari a gasar spelling Bee da aka gudanar a birnin Damaturun jihar Yobe, sai dai kash, a kusa da ƙarshe ya yi rashin nasara. Nan da nan yaro ya ke sharɓar kuka, ana ta lallaɓarsa amma ya ƙi ya yi shiru.

Daga baya an tambaye shi dalilin kukan, sai ya ce an masa alƙawarin idan har ya ci gasar za a saya masa keke.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina saboda halin rashin ɗa’a

To kuma ga shi bai ci gasar ba. Kenan ba za a saya masa wannan keke da ya ke shauƙi da buri ba.

A lokacin da Farfesa Ali Ibrahim Abbas ya ji wannan labari, shi ne ya ƙira yaron, aka je aka sayo masa sabon keke aka ba shi. Ta ke yaro ya hau murna da farin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here