Trump yana jinya a asibiti bayan da aka ji masa rauni wajen yaƙin neman zaɓe

0
46
Trump yana jinya a asibiti bayan da aka ji masa rauni wajen yaƙin neman zaɓe

Trump yana jinya a asibiti bayan da aka ji masa rauni wajen yaƙin neman zaɓe

Ofishin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, tsohon Shugaban ƙasar ya samu rauni a fuska a ranar Asabar, amma yana “lafiya” bayan da aka harba bindiga a wajen da ya ke wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Pennsylvania.

Ofishin yaƙin neman zaɓen Trump ya ce ana kulawa da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar Republican a wani asibiti da ke garin Butler.

Trump ya je garin Butler da ke ɗaya daga cikin jihohin da ba su da tsayyen ɗan takara, domin gudanar da wani taro.

Kakakin ofishin yaƙin neman zaɓen Tump Steven Cheung ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa, “Shugaba Trump ya godewa jami’an tsaro da jami’an agajin gaggawa saboda ɗaukar mataki nan da nan yayin wannan ɗanyen aikin, yana lafiya kuma ana duba lafiyarsa a wani asibitin gida.”

KU KUMA KARANTA:Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Mutane sun ji ƙara masu kama da harbin ƙananan bindigogi kafin tsohon Shugaban ya kama gefen fuskarsa ya noƙe a bayan dogon teburin da yake tsaye yana magana. Nan da nan jami’an leƙen asiri suka yi wuf suka kakkange shi. Ana jin yana cewa “bari in ɗauko takalmina,” kafin ya miƙe tsaye, jami’an leƙen asiri suna kewaye da shi.

An ga jini yana kwarara daga kunnensa na dama, ya kuma yi ta cewa, akai-akai, ” jira.” Daga nan ya ɗaga hannu na dama ya tsira hannu yana nuna tsakiyar taron ya maimaita kalma guda ɗaya sau uku.

Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leƙen asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Wannan yanzu bincike ne na ma’aikatar tsaron, kuma za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.”

Fadar White House ta aikawa manema labarai wata sanarwa cewa, Shugaba Joe Biden “ya sami bayanin farko game da abin da ya faru a taron tsohon Shugaba Trump.” Bayan ‘yan mintoci kaɗan, su ka ce manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da shugaban hukumar leƙen asiri, da manyan hadimai da kuma sakataren tsaron cikin gida su na yi wa Shugaban ƙasar bayani a kan lamarin.

Ofishin Mataimakiyar Shugaban ƙasar kuma ya shaida wa manema labarai cewa, ana yi wa Mataimakiyar Shugaban ƙasar bayanin farko.

Babban Lauyan ƙaramar Hukumar Butler, Richard Goldinger ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa, dan bindigar da ake zargin ya mutu, kuma an kashe aƙalla mutum guda daga cikin waɗanda su ka halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here