No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan sanda a Kano sun ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano, ta ceto wata yarinya ‘yar shekara biyu mai suna Amina da wani maƙocinsu, Zakariyya Muhammad, ya sace ta a unguwar Sabuwar Ganduje da ke jihar.

Maƙocin ya nemi kuɗin fansa Naira miliyan biyu kafin ya sako yarinyar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, ta ce wani mazaunin Sabuwar Gandu Kwarin Barka ne ya sanar da faruwar lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Salman Dogo Garba, ya tura tawagar yaƙi da garkuwa da mutane, inda suka kama wanda ake zargin cikin sa’o’i 24.

Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an leƙen asirin sun yi nasarar cafke wanda ake zargin mai Zakariyya Muhammad, mai shekara 22 wanda mazaunin Sabuwar Gandu Kwarin Barka ne.

KU KUMA KARANTA: An ceto ɗaliban jami’ar Jihar Kogi da aka sace

Sanarwar ta ce matashin ya amsa aikata laifin shi kaɗai, sannan ya jagoranci ’yan sanda zuwa inda ya ɓoye yarinyar.

An ceto Amina sannan an garzaya da ita asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed da ke Kano, inda aka duba lafiyarta, sannan aka sallame ta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya yi kira da mazauna jihar da su kai rahoto ga ‘yan sanda a duk lokacin da suka zargi wani abu na tafiya ba daidai ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...