Kotun duniya ta umurci Isra’ila ta dakatar da kai farmaki a Rafah

1
176

Kotun duniya ta umurci Isra’ila ta dakatar da kai farmaki a Rafah

A ranar Juma’a ne babban kotun duniya ICJ ta umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-haren da take yi a Rafah, birnin da ke kudancin Gaza inda Falasɗinawa sama da miliyan ɗaya suka nemi mafaka a cikin mawuyacin hali.

Ko da yake da wuya Isra’ila ta bi wannan umarni, wanda babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta da hurumin aiwatar da shi, amma hukuncin da aka yanke zai ƙara matsin lamba kan ƙasar.

A ci gaba da ƙalubalantar ɓacin ran da ƙasashen duniya suka yi kan rikicin jin kai a yankin, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai munanan hare-haren da suka ƙaddamar sakamakon hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

KU KUMA KARANTA:Babbar Kotun MƊD ta fara sauraron ƙara kan afka wa Rafah da Isra’ila ta yi

Tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura, duk da matsin lamba da ake yi a gida na firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na ganin an sako mutanen da a ka yi garkuwa da su a Gaza.

Umurnin na ICJ ya biyo bayan roƙon gaggawa da ƙasar Afirka ta Kudu ta gabatar a wani ɓangare na shari’ar da take ci gaba da yi a kotun da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands, inda ta zargi Isra’ila da aikata kisan kiyashi a hare-haren da ta shafe watanni ana kai wa Gaza, zargin da Isra’ila da Amurka suka musanta.

Mai yiyuwa ne shari’ar za ta ɗauki shekaru ana warwarewa, amma Afirka ta Kudu ta nemi umarnin wucin gadi don kare Falasɗinawa.

1 COMMENT

Leave a Reply