Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II Sarautar Kano

0
68
Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II Sarautar Kano

Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II Sarautar Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II sarautar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar Kano kai tsaye ranar Alhamis, jim kadan bayan ya sa hannu kan gyaran dokar Masarautun Kano ta 2024 da majalisar dokokin jihar ta yi da safiyar Alhamis.

Gwmnan na Kano ya bayyana cewa hakan na nufin a yanzu a wannan jiha “sarki ɗaya tilo muke da shi.”

“Wannan yana nufin wannan sarki shi zai ci gaba da riƙe ragama ta masarautarmu ta Kano baki ɗayanta,” a cewar Gwamna Abba, a jawabin da aka watsa kai tsaye ta kafofin watsa labarai na Kano da kuma shafukan sa da zumunta.

“Kowa ya riga ya san cewa bisa waccan doka ta baya wacce suka rusa suka lalata, Sarki Malam Muhammadu Sanusi Aminu Sanusi shi ne sarki a wancan lokaci.”

Gwamnan ya ƙara da cewa “saboda haka bisa canji da aka yi na wannan doka, a yau nima na yarda, majalisa ta yarda, an dawo da Mai Martaba Malam Sanusi Lamiɗo Aminu Sanusi wannan kujera ta Sarkin Kano.”

Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Majalisar Dokokin Jihar ta Kano ta amince da gyaran dokar Masarautun Kano ta 2019, wacce ta yi sauye-sauye da dama kan masarautar Kano inda ta ƙirƙiri ƙarin masarutu huɗu maso daraja da ɗaya.

READ ALSO: Majalisar Dokokin Kano ta amince a rusa Masarautu 4 da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙira

Gyaran dokar da majalisar ta yi a wannan makon ya soke duka sauye-sauyen da aka yi a baya, aka kuma koma amfani da tsohuwar dokar masarautu.

Sabuwar dokar ta 2024 ta fara aiki ne a ranar Alhmis bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa mata hannu.

A lokacin da yake yi wa al’ummar Kano jawabi, gwamna Abba Kabir ya umarci sarakunan Kano biyar a tsohuwar gwamnatin Ganduje ta naɗa da su fice daga gidajen sarauta, tare da miƙa duka kayan sarauta ga kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar.

“Ina so saboda wannan, na yi kira ga sauran sarakuna, waɗana wannan doka da aka cire ta shafa, cewar su yi ƙoƙari su bar gidan gwamnati cikin awa 48 su tabbatar da cewa sun bar gidan gwamnati, sun bar fadar sarki da ofisoshinsa,” kamar yadda ya faɗa.

Ya kuma umarci tuɓabbun sarakunan su gaggauta miƙa wa Mataimakin Gwamnnan Kano wanda shi ne kwamishinan ƙananan Hukumomin jihar takardun barin aiki.

A ranar 9 a watan Maris ɗin 2024 ne gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ta sauke Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano saboda wasu dalilai da gwamnatin lokacin ta zargi shi da su.

Dalilan sun haɗa da zargin rashin biyayya ga gwamnati, da zargin shiga siyasa, da zargin sukar manufofin gwamnati, da son ‘kare martabar Kano’, kamar yadda gwamnatin ta bayyana a lokacin.

Leave a Reply