Sojin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo sun daƙile yunƙurin juyin mulki

0
47

Sojin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo sun daƙile yunƙurin juyin mulki

Jamhuriyar Dimokaraɗiyar Congo ta ce ta daƙile wani yuƙurin   kifar da gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi a Kinshasha, kuma har da ƴan  ƙasashen waje a cikin masu wannan yunƙuri.

Lamarin ya auku ne da safiyar Lahadi a kusa da gidan ministan tattalin arzikin ƙasar, Vital Kamerhe, a yankin Gombe da ke arewacin babban birnin ƙasar, kamar yadda rahotanni  suka bayyana.

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar ƙasar, kakakin rundunar sojin ƙasar, Janar Sylvain Ekenge ya tabbatar da lamarin, inda ya ce an kashe jagoran masu yukurin juyin mulkin, tare da kama mutane 50 da ke da hannu a ciki da suka haɗa  da wasu Amurkawa da dama da wani ɗan Birtaniya guda.

KU KUMA KARANTA:Da gaske ne an yi yunƙurin juyin mulki a Congo Brazzaville?

Janar Ekenge ya ce ɗan ƙasar Congon da ya jagoranci yunƙurin kifar da gwamnatin shine, Christian Malanga, wanda ya ke da takardar zaman ɗan Amurka, kuma tuni dakarun Congo su ka kashe shi.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa an ji ƙararraƙinharbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar a lokacin yunƙurin juyin mulkin.

Jakadan Amurka a Kinshasha ya bayyana kaɗuwarsa a kan lamarin da ya auku, a yayin da Tarayyar Afrika ta caccaki yunƙurin na kifar da gwamnatin farar hula.

Masu yunƙurin juyin mulkin sun shirya kai farmaki gidan sabuwar fira ministar ƙasar, Judith Suminwa, da kuma na mministan tsaro, Jean-Pierre Bemba, amma kuma sai suka gaza gane gidan Suminwa.

Leave a Reply