No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya ce kayayyakin abincin da gwamnati take saya don rabawa mabuƙata na daga cikin dalilan da suke ƙara hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Cardoso ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kwamitin da ke bibiyar tsare-tsare da hada-hadar kuɗaɗe, wanda aka wallafa rahoton watan Maris a shafin babban bankin na CBN a ranar Litinin a cewar gidan talabijin na Channels.

A taron ne kwamitin ya ƙara adadin kuɗin ruwa daga 22.75 zuwa 24.75, matakin da kwamitin ya ce ya ɗauka don karya tagomashin matsalar hauhawar farashin na kayayyaki.

KU KUMA KARANTA:Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Sai dai tsarin yadda mutane ke sayen kayayyaki da Hukumar Ƙididdiga ta Nigerian Bureau of Statistics ta fitar (NBS) a watan Afrilu, ya nuna cewa matsalar hauhawar farashin kayayyakin ta ƙaru zuwa kashi 33.2 a watan Maris.

Tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 40.01, inda yakan ƙaru a kowace shekara zuwa 15.56 daga kashi 24.45 watan Maris ɗin 2023.

Cardoso ya ƙara da cewa, duk da matakan da aka ɗauka don magance matsalar ta hauhawar farashin kayayyakin lamarin ya ƙi sauyawa duk da daidaito da aka samu a farashin canjin kuɗaɗen waje.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...