Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza

Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar ɗaliban da ke zanga-zangar adawa da hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza.

Jami’ar ta ce ɗaliban da ke zaman dirshan a wani ginin harabar makarantar a matsayin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu, na fuskantar korar daga karatunsu, saboda sun karya doka.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibai a faɗin Amurka na ci gaba da yin zanga-zangar nuna adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza

“Ɗaliban da suka mamaye ginin na fuskantar kora,” in ji ofishin kula da harkokin jama’a na Columbia a cikin wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa an ba masu zanga-zangar “damar fita cikin lumana” amma a maimakon haka suka ƙi tare da kara ta’azzara lamarin.

Ana kallon wannan a matsayin keta hakkin ɗaliban da ƙoƙarin hana su faɗin albarkacin bakinsu a ƙasar da take iƙirarin kare ƴancin ɗan’adam.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *