Wannan gobara ta tankar mai ta yi matuƙar kaɗa mu – Gwamna Fubara

0
207

Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara, ya kwatanta gobarar da ta tashi a jikin wata tankar mai a birnin Fatakwal na jihar Rivers a kudancin Najeriya a matsayin mummunan al’amari da ya kaɗa al’ummar jihar.

Fubara ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gane wa idonsa da ya kai East-West Road da lamarin ya faru a daren Juma’a inda wata tankar mai ta kama da wuta ta halaka mutane tare da ɓarnata dukiyoyi da dama.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito gwamna Fubara yana cewa mutum biyar ne suka mutu yayin da motoci 120 suka ƙone.

KU KUMA KARANTA:Mutane da dama sun mutu, sakamakon fashewar tankar mai a Fatakwal

“Wannan gobara ta matuƙar taɓa zukatanmu, mun ji zafinta, musamman duba da cewa abu ne da za a iya kaucewa da a ce ana bin ƙa’idojin kiyaye haɗurra.

“Muna miƙa saƙon jajenmu ga waɗanda ibtila’in ya rutsa da ‘yan’uwansu, da motocinsu da sauran kadarori.

“Za mu duba hanyoyin da za mu ci gaba da taimakawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa.” Fubara ya ce a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

Motar tankar man wacce rahotanni suka ce ta kama da wuta da misalin ƙarfe 9:45 na daren Juma’a ta shafi motoci da dama da ke cikin cunkoson ababen hawa.

Leave a Reply