Sanarwar da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar tace, an warware matsalar.
Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya bayyana cewar matsalolin tsare-tsare ne suka sabbaba dawowar dogayen layukan mai a wasu sassan ƙasar.
Sai dai sanarwar da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar tace, an warware matsalar.
KU KUMA KARANTA:NNPC ta ƙara farashin man fetur a Najeriya
Sanarwar tace, “babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, na so ya bayyana cewar matsalolin tsare-tsare ne suka sabbaba matsalar ƙarancin man fetur da ake fama a wasu sassan ƙasar nan a halin yanzu, kuma an riga an magance ta.
“Kuma kamfanin yana son jaddada cewar farashin albarkatun man fetur na nan a yadda suke ba su sauya ba.”
Don haka NNPCL na ƙira ga ‘yan Najeriya da su kaucewa ɗabi’ar ɓoye man, kasancewar akwai wadatarsa a ƙasar”.