Tallafawa dukkan jiragen dake tafiya ƙasashen waje zai haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya – Masana

0
358

A yayin da alƙaluma suka yi nuni da cewa wasu kamfanonin jiragen saman waje sun shiga takun saƙa da kamfanin Airpeace, hukumar kula da ƙungiyoyin fararen hula ta Najeriya NCSCN da wasu masana tattalin arziƙi sun buƙaci gwamnati ta tallafawa kamfanin na cikin gida.

Kama daga ɗauke harajin shekara guda ganin halin da ‘yan Najeriya ke shiga na tsadar farashin tikitin tafiya ƙasashen waje.

Babban Daraktan hukumar kula da ƙungiyoyin fararen hula ta Najeriya wato NCSCN, Blessing Akinlosotu, ya ce ƙasa da mako guda da kamfanin jirgin saman jigilar fasinjoji na Air Peace ya shiga babin tafiya Landan daga Legas a kan Naira miliyan ɗaya da ɗoriya, kamfanin jirgin saman Birtaniyya da ke tafiya a kan wannan hanyar ya rage farashinsa daga Naira miliyan 3 zuwa ƙasa da Naira miliyan ɗaya cikin kwanaki 3 kacal lamarin da ƙungiyoyin ke gani a matsayin yiwa Airpeace zagon ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Ambaliyar ruwa ta kawo gagarumin tsaiko a sufurin jiragen sama a Dubai

Ganin yadda fara jigilar fasinjoji zuwa Ingila na kamfanin Airpeace ya fara yin tasiri ga rage farashin tikitin wasu kamfanonin jiragen saman ƙasashen waje, baya ga ci gaba da farfaɗowar darajar Naira ga kuma batun fara sayar da man jirgin sama da matatar man kamfanin Dangote ke yi a yanzu, ya sa muka tuntuɓi wasu ‘yan Najeriya ko waɗannan matakan sun kawo sauƙi ga farashin tikitin zirga zirga a cikin ƙasar kuma akasarin waɗanda muka tuntuɓar suka ce ba wannan maganar.
Kungiyoyin fararen hula dai sun yi kira ga gwamnati da ta ba wa kamfanin Airpeace kariya, dauke masa harajin shekara 1 la’akari da rangwamin farashin da ‘yan kasashen waje ke cin moriya a nasu kasashen kamar yadda darakta a kungiyar NCSCN, Alhaji Gambo Haruna Jagindi ya bayyana.

A wani ɓangare kuwa, masanin tattalin arziƙi, Mallam Kasim Garba Kurfi ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta duba ta taimakawa kamfanonin jiragen saman ƙasa dake zirga-zirga zuwa ƙasashen waje wanda zai taimakawa ƙasar samun kuɗaɗen shiga.

Duk ƙoƙarin ji ta bakin gwamnatin tarayya ta ɓangaren ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama a kan yiyuwar ɗaukewa kamfanin Airpeace haraji na tsawon shekara guda ta ƙiran wayar tarho da saƙon karta kwana ya ci tura a yayin haɗa wannan rahoton.

An daɗe ana kai ruwa rana tsakanin kamfanonin jiragen saman ƙasashen waje da na cikin gida Najeriya a kan gogayya ta fuskar rage farashi da zarar ƙasar ta ɗan yunƙuro saboda haka kamata ya yi gwamnati ta dage a wannan karon ganin ba a ture Airpeace daga kasuwancin jigila ba in ji masana.

Leave a Reply