Babban Hafsan Sojojin Kenya, Francis Ogollaya, ya mutu a hatsarin helikwafta

0
172

Babban hafsan sojin ƙasar Kenya Janar Francis Ogolla na daga cikin manyan kwamandojin da suka mutu a lokacin da wani jirgin yaƙi mai saukar ungulu ya yi hadari a yammacin ƙasar, kamar yadda wani jami’in diflomasiyya da majiyar gwamnati suka bayyana.

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin Kenya dauke da manyan hafsoshin soji ya faɗi a gundumar Elgeyo Marakwet, mai tazarar kilomita 400 daga arewa maso yammacin Nairobi babban birnin ƙasar a ranar Alhamis, kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Jirgin helikwafta ya kama da wuta bayan da ya fado, kuma akwai manyan kwamandoji sama da 10 ciki har da Janar Ogolla,” in ji jami’in.

“Sun je yankin ne domin aikin tsaro saboda akwai sojojin KDF (Dakarun tsaron Kenya) da aka girke a yankin,” in ji shi.

Bayan da aka samu labarin faɗuwar jirgin, Shugaba William Ruto ya kira taron gaggawa na kwamitin tsaron ƙasar, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

KU KUMA KARANTA: Mutum 3 sun rasu, an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe

“Shugaba William Ruto ya ƙira wani taron gaggawa na kwamitin tsaron ƙasa a fadar gwamnatin Nairobi da yammacin yau, bayan wani hatsarin helikwafta da sojojin Kenya suka yi da yammacin yau a gundumar Elgeyo-Marakwet,” in ji kakakin fadar gwamnatin ƙasar Hussein Mohamed a cikin wata sanarwa.

Akalla sojoji goma ne suka mutu a watan Yunin 2021 lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi haɗari a lokacin da yake sauka kusa da babban birnin ƙasar Nairobi.

Babban Hafsan Dakarun Kenya Janeral Francis Ogolla ya mutu ranar Alhamis yana da shekara 62, kamar yadda Shugaba William Ruto ya tabbatar.

“Na yi jimamin sanar da mutuwar Janar Francis Omondi Ogolla Babban Hafsan Dakarun Kenya,” kamar yadda Ruto ya sanar a wani jawabi da yayi a ranar Alhamis da daddare, inda ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a faɗin ƙasar.

Ogolla na cikin mutum 11 dake cikin helikwaftan na sojoji da ya yi hadari kuma ya kama da wuta a yankin Sindar da ke iyaka da yankin Elgeyo a arewa maso yamma da kuma Pokot to Yamma da 2:20 na rana.

Mutum tara sun mutu nan take, yayin da biyu suka ji raunuka, kuma ana dauke su a jirgi zuwa babban birnin kasar Nairobi don yi musu magani.

Shugaba Ruto ya naɗa Ogolla a matsayin Hafsan Dakarun Kenya a ranar 28 ga watan Aprilun 2023, inda maye gurbin Robert Kibochi, wanda ya cika shekarun ritaya.

Leave a Reply