Kasar Mali ta sanar da cewa za ta fara sayen man dizel daga makwabciyarta Nijar a wani yunƙuri na bunƙasa ɓangaren samar da wutar lantarkin ƙasar.
Ana sa ran Nijar za ta samar da litar dizel miliyan 150 ga makwabciyarta Mali a tashoshin samar da wutar lantarkin kasar wacce take fama matsalar lantarki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Mali ta bayyana ranar Talata.
Kimanin mutum miliyan 11 wato rabin al’ummar ƙasar ne ke samun lantarki a kasar wacce take karkashin mulkin soja tun juyin mulkin da aka yi a kasar a shekarar 2020.
Ana bin kamfanin makamashin ƙasar (EDM-SA) CFA biliyan 200 (dala miliyan 330) kuma ba ya iya samar da lantarki a babban birnin kasar Bamako da sauran biranen Mali.
Jagoran gwamnatin Mali Kanal Assimi Goita ya gana da Ministan Man Fetur na Nijar Mahaman Moustapha Barke don fitar da matsaya “kan yarjejeniyar sayar wa Mali man dizel lita miliyan 150,” kamar yadda fadar shugaban Mali ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
“Wannan man dizel din za a kai shi kamfanin Energie du Mali (EDM-SA) don rarraba shi ga tashoshin lantarkin ƙasar,” kamar yadda Barke ya bayyana a wata sanarwa.
KU KUMA KARANTA: Ɗangote ya karya farashin dizel zuwa N1,000 kan kowace lita
A watan Fabrairu, Nijar ta sanar da ƙulla wata yarjejeniya ta samar da man dizel ga kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Chadi, wadanda duka kasashe ne da yanzu suke karkashin mulkin soji.
Kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali sun kulla wani sabon kawance da suka kira Alliance of Sahel States (AES), kuma a watan Fabrairu sun sanar da fita daga kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS.
Kazalika gwamnatin Nijar ta ƙaddamar da wani bututun mai a watan Nuwamba wanda zai rika daukar danyen man fetur din da aka hako daga matatar mai ta Agadem da ke kudu maso gabashin kasar zuwa makwabciyar ƙasar Benin.
Kamfanin China National Petroleum Corporation (CNPC) mallakin kasar China ne yake hako man fetur din.
Mahukunta a Nijar sun ce a ranar 13 ga watan Afrilu sun samu rancen dala miliyan 400 daga China a matsayin “lamuni” na samar mata da danyen man, wanda za a fara sayar da shi a watan Mayu.
Ƙasar tana da shirin ƙara yawan man fetur ɗin take samarwa zuwa ganga 110,000 a kowace rana, inda za a rika fitar da ganga 90,000.