Mahara sun kai farmaƙi sakatariyar gwamnatin jihar Oyo

0
110

Jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin, tare da kama wasu daga cikin waɗanda suka kai farmaƙin.
Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin sakatariyar Gwamnatin Jihar Oyo, inda suka yi yunƙurin ƙwace iko da ofishin gwamna da kuma majalisar dokokin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar ana zargin maharan sun yi ƙoƙarin ƙwace iko tare da kafa tutar Ƙasar Oduduwa a gidan gwamnatin jihar.
Wani ganau, ya ce maharan na sanye da kayan aikin soja, sannan sun rufe fuskokinsu da wani ƙyalle.

Majiyar ta ce jami’an ’yan sanda da haɗin gwiwar dakarun Amotekun ne suka yi ɗauki-ba-daɗi da maharan.

Rahotanni sun ce maharan sun isa sakatariyar ne cikin motoci ƙirar bas, ɗauke da wata tuta da ke nuni da suna rajin kafa wata ƙasa ne.

Mutanen da ke kusa da sakatariyar sun jiyo ƙarar harbe-harbe bindiga na tsawon lokaci.

KU KUMA KARANTA:An sake rufe wasu asibitocin bogi 6 a jihar Oyo

An tura ƙarin jami’an tsaro da yawa ciki har da sojoji, inda suka mamaye sakatariyar, tare duk wasu ƙofofin shiga da fita na sakatariyar.
An sauya wa ababen hawa da ke zirga-zirga daura da sakatariyar zuwa wata hanya.

Jami’an tsaro sun kama wasu a yayin harin, amma har yanzu ba su tabbatar da adadin mutanen da suka kama ba.

Majiyoyin sun ce an yi nasarar kama wasu daga maharan ne, biyo bayan taho-mu-gama da suka yi da jami’an tsaro.

Leave a Reply