No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata kotun Afirka ta Kudu ranar Talata ta amince tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ya tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Mayu.

Kotun ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗauka na haramta wa Mr Zuma tsayawa takara saboda samunsa da laifi a baya.

Kotun ta ce Zuma, mai shekara 81, zai iya tsayawa takara duk da yake yana goyon bayan jam’iyyar hamayya ta Mkhonto we Sizwe (MK), wadda ake ganin za ta taka rawa a zaɓen.

“An yi watsi da matakin Hukumar Zaɓe,” in ji hukuncin da kotun ta yanke wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani.

KU KUMA KARANTA: An haramtawa Jacob Zuma tsayawa takarar shugaban ƙasa a Afrika ta Kudu

Ba ta yi ƙarin bayani ba game da dalilan yanke hukuncin.

Ranar 29 ga watan Mayu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Afirka ta Kudu wanda masu sharhi ke gani zai kasance mafi zafi tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1994.

Damar da Zuma ya samu ta tsayawa takara za ta iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓen.

Ana sa rai jam’iyyar MK za ta samu tagomashi saboda goyon bayan da Zuma yake ba ta, kuma tana iya samun ƙuri’u a mahaifarsa waɗanda a baya jam’iyyar African National Congress (ANC) take buga ƙirji da su.

Hakan ka iya sanyawa ANC ta sha kashin da ba ta taɓa fuskanta ba a shekarun talatin da ta kwashe tana mulki, kuma tana iya rasa kaso 50 na ƙuri’un da ake buƙata don kafa majalisar dokoki

Tun da farko hukumar zaɓen kasar ta haramta wa Zuma tsayawa takara, inda ta ce kundin tsarin mulkin ƙasar bai amince mutumin da aka yanke wa hukunci har ya yi zaman gidan yari na wata 12 tsayawa takara ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...