Mutum fiye da 90 ne suka mutu yayin da wani kwale-kwale maƙare da jama’a ya kife a arewacin Mozambik, a cewar hukumomi ranar Lahadi.
Kwale-kwalen, wanda na kamun kifi ne ɗauke da mutum aƙalla 130, ya kife ne a lokacin da yake ƙoƙarin isa wani tsibiri da ke lardin Nampula, in ji wasu jami’an gwamnati.
Sakataren jihar Nampula, Jaime Neto ya ce, “Ya nitse ne sakamakon lodin da aka yi masa wanda ya wuce ƙima. Fasinjoji 91 ne suka mutu.”
Ya ƙara da cewa ƙananan yara da dama na cikin waɗanda suka mutu.
Masu aikin ceto sun kuɓutar da mutum biyar da ransu kuma suna ci gaba da neman ƙarin mutanen da lamarin ya shafa, amma suna fuskantar ƙalubale sakamakon rashin yanayi mai kyawu.
Neto ya ce akasarin mutanen da ke cikin kwale-kwalen suna ƙoƙarin tserewa daga yankin ne sakamakon wani labarin ƙarya da aka riƙa yaɗawa cewa cutar kwalara ta ɓarke a yankinsu.
KU KUMA KARANTA: Mutane 20 sun mutu a wani kwale-kwale da ya nutse a gaɓar tekun Senigal
Bayanan da gwamnatin Mozambik ta fitar sun nuna cewa mutum kimanin 15,000 ne suka kamu da cutar kwalara inda 32 daga cikinsu suka mutu tun daga watan Oktoba.
A watannin baya-bayan nan, mutane sun riƙa tserewa zuwa yankin na Nampula sakamakon hare-haren ƴan bindiga da suke fuskanta a yankin Cabo Delgado da ke maƙwabtaka.
Neto ya ce an soma gudanar da bincike don gano musabbabin kifewar kwale-kwalen.
Ya ƙara da cewa biyu daga cikin mutanen da aka ceto suna samun kulawa a asibiti.