Shirin gwamnatoci na ciyar da mabuƙata a watan Ramadan na cin karo da ƙalubalen zargin almundahana

0
145

Yayin da al’ummar musulmi ke daf da kammala ibadar Azumin Ramadana, aiwatar da shirin gwamnatoci na ciyar da mabuƙata a cikin wannan wata na cin karo da ƙalubalen zargin almundahana, inda ake tuhumar wasu daga cikin Jami’an gwamnati da hannu.
Irin wannan zargi dai ya sanya gwamnan jihar jigawa Umar Namadi dakatar da guda daga cikin kwamishinonin sa tare da ba da umarnin gudanar da binciken ƙwaƙwaf.

Cikin wata sanarwa a jiya wadda sakataren gwamnatin Jigawa Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman Umar Namadi ya ba da umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Aminu Kanta saboda zarginsa da hannu wajen almundahanar a tsarin aiwatar da Shirin gwamnatin jihar na ciyar da mabuƙata a wannan wata na Ramadana.

Comrade Salisu Mazge Gumel guda cikin jagororin ƙungiyoyin ci gaba da al’umma a Jigawa yana bibiyar yadda gwamnatin jihar ta Jigawa ke aiwatar da wannan shirin na ciyarwa, la’akari da ɗaruruwan miliyoyin naira da gwamnatin ta keɓewa tsarin.

“Akwai ƙumbiya-ƙumbiya a cikin harkar, yanzu za ka baiwa mace wake kwano goma, Gero kwano 10, shinkafa kwano 10, amma babu wanda zai tsaya ya tabbatar da cewa, wannan adadi an dafa shi, baya ga haka ‘yan kwangilar dake rarraba kayan ga masu dafawar babu wanda zai sanya masu idanu ya tabbatar da cewa, ya ba da adadin da ya kamata ya baiwa masu dafawa.”

A jihar Kano ma dake maƙwabtaka da Jigawan, irin wannan badaƙalar gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf ya gano a tsarin ciyar da mabuƙata na gwamnatin sa a cikin wannan wata mai alfarma.

KU KUMA KARANTA:Muƙarraban Ganduje sun mayar da martani kan kwamitin da Gwamnan Kano ya kafa na binciken tsohon gwamnan

Kimanin naira biliyan biyu gwamnatin ta keɓewa shirin, amma a wata ziyarar ba za ta gwamnan ya nuna rashin gamsuwa da nau’in abincin da ake baiwa talakawa.

Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ne Daraktan yaɗa labaru na gwamnan yace, “Mai girma gwamna ya kewaya da kansa da ya daga cikin cibiyoyin da ake wannan aiki kuma ya ga abin da ake yi ya saɓa da umarnin da ya bayar, wanda haka ta sanya ya ba da umarnin cewa, tilas ne a canza wannan tsari kuma ayi bincike domin ɗaukar mataki.”

Yanzu dai kusan makonni biyu kenan da suka shuɗe amma har yanzu babu labarin dangane da irin matakin ladaftarwa da gwamnan ya ɗauka akan waɗanda yace suna yi masa zagon ƙasa.

Dakta Kabiru Sa’idu Sufi, mai sharhi akan harkokin gwamnati da lamuran yau da kullum yace, “Wannan yana nuna ta’azzara ne na cin hanci da rashawa da almundahana, musamman akan abubuwan da suka shafi ayyukan gwamnati.”

Wannan zargin almudahana a tsakanin Jami’an gwamnati na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da ƙalubalen tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.

Leave a Reply