No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jagoran ‘yan’uwa Musulmi a Kaduna da aka fi sani da ‘yan Shi’a ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Elzakzaky, Malam Aliyu Umar Tirmidhi ya shaida wa BBC cewa ‘yansanda sun auka musu tare da buɗe musu wuta ba tare da wani dalili ba, inda suka kashe mutum biyar da jikkata 25, a lokacin da suke gudanar da Muzaharar nuna goyon baya ga Falasɗinawa jiya Juma’a, a birnin Kaduna.

“Muna cikin muzaharar lami lafiya kawai sai muka ji ana harbe-harbe a bayanmu. Hakan ya sa muka yi addu’a muka ce kowa ya tafi gida. Ai kuwa kawai ‘yansanda suka ƙara buɗe wuta inda suka shahadantar da mutum biyar da jikkata 25.”

Mabiya Shaikh Zakzaky dai kan gudanar da muzaharar nuna goyon baya ga Al’ummar Falasɗinawa a duk juma’ar ƙarshen watan Ramadan.

KU KUMA KARANTA: An kama mutum 8 kan zargin kashe malami a Jami’ar Maiduguri

Malam Tirmidhi ya kuma ce a Zariya ma ‘yansandan sun harbe mutum ɗaya ya kuma ya yi shahada.

Dangane kuma da waɗanda aka kama, malam Tirmidhi ya ce yanzu haka suna haɗa alƙaluman domin tantance yawansu amma dai sun haƙƙaƙe cewa a yanzu mutum shida suna hannun ‘yansanda.

Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna dai ta bakin mai magana da yawunta, ASP Mansir Hassan, ta ce “mutanen sun fito ɗauke da makamai kuma suka far wa al’ummar gari wannan ya sa muka tarwatsa su sannan mun kama wasu za mu gurfanar da su a kotu.”

To sai dai malam Tirmidhi ya ce wannan maganar ba gaskiya ba ne.

“Mu da muka fito mata da maza sannan ƙanana da manyanmu wato ƙwanmu da ƙwarƙwata yaya za a yi mu ɗauki makami har mu fara far wa jama’a? Ai hankali ba zai ɗauka ba.”

Tuni dai har an yi jana’izar waɗanda ‘yansandan suka kashe kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...