No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta’addanci a Katsina da Zamfara sun kai jerin samame a maɓoyar ƴan ta’adda inda suka kashe da dama daga cikinsu.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da safe.

Kazalika ta ce dakarunta sun kama tarin miyagun ƙwayoyi a hannun wasu masu fasa-ƙwauri a jihar Ogun da ke kudancin ƙasar kuma za ta miƙa su ga hukuomin da suka dace.

“A samamen da suka kai Zamfara ranar 29 ga watan Maris, dakarunmu sun yi nasarar far wa maɓoyar gawurtaccen ɗan ta’adda, Hassan Yantagwaye, a ƙaramar hukumar Tsafe.

Yantagwaye da tawagarsa ne suka yi garkuwa da mutane da dama tare ta’addanci a wasu yankuna Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Yayin samamen, dakarun sun yi luguden wuta a kan ta’adda bayan sun yi musayar harbe-harbe, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da ƙwace makamai da dama,” in ji sanarwar.

Kazalika ranar 30 ga watan Maris, dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindiga a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Faskari da ke Katsina.

“Dakarun sun kashe ƴan ta’adda 8 tare da ƙwato bindigogi uku ƙirar-gida, da kakin soji da hatsi mai yawa,” a cewar sanarwar.

Haka kuma sojojin Najeriya sun ce sun kai samame da daddare a wani yanki na ƙaramar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi ranar 31 ga watan Maris inda suka gamu da mayaƙan ƙungiyar tsageru ta Effium.

Dakarun sun murƙushe tsagerun inda suka kama ɗaya daga cikinsu. Kazalika dakarun sun ƙwace bindiga samfurin AK – 47 da alburusai kuma “yanzu haka ana gudanar da bincike kan mutumin da aka kama.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...