No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kamfanin dillancin labaran Isra’ila ya rawaito cewa Firaminista Benyamin Netanyahu ya bayar da umarnin sayen tantuna 40,000 daga kasar Chaina da za a kafa a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, a shirye-shiryen kai farmaki ta kasa a Rafah inda Falasɗinawa sama da miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Netanyahu ya yi watsi da fargabar da duniya ke da shi na fuskantar bala’in jinƙai idan Isra’ila ta kai farmaki ta ƙasa a yankin kudancin Gaza, yana mai cewa fararen hula za su iya tserewa faɗan zuwa wasu sassan yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Da yake magana da tawagar majalisar dokokin Amurka da ke ziyara a Isra’ila, Netanyahu ya ce mutanen da ke mafaka a Rafah – fiye da rabin al’ummar Gaza miliyan 2.3 – za su iya ficewa daga faɗan.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta musanta zargin da ake mata na alaƙa da Isra’ila

“Kawai mutane su tafi, su tafi da tantunansu,” in ji Netanyahu a cikin kalamansa na izgilanci. “Mutane sun koma Rafah. Suna iya sake barin can ɗin ma.”

Kutsen da Isra’ila ke shirin yi ya tayar da hankulan duniya saboda birnin, wanda ke kan iyakar Gaza da Masar yana cunkushe da Falasɗinawa sama da miliyan 1.5 a sansanoni da tantuna da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa, waɗanda galibinsu suka tsere daga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa wasu wurare.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...