Dakarunmu ba za su bar yankin Neja-Delta ba har sai an kamo waɗanda suka aikata kisan gillar – Rundunar Soji

0
124

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta ba za su bar yankin Neja-Delta ba har sai an kama waɗanda suka yiwa dakarunta 17 kisan gilla.
Kisan gillar da aka yiwa sojojin a makon da ya gabata a yankin Neja-Delta a wani al’amarin da ya jefa rundunar sojin Najeriya cikin garari ya janyo cece kuce a faɗin Najeriya.

An ƙone ƙauyen Okuama dake ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta inda al’amarin ya faru, sakamakon kisan gillar, abin da ya ƙara fargabar harin ramuwar gayya daga sojojin.

Sai dai babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ta 6 ta haɗin gwiwa dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin kudu maso kudancin ƙasar nan me taken: “Operation Delta Safe” a turance, Manjo Janar Jamal Abdussalam ya baiwa shugabannin Neja-Delta tabbacin cewar dakarun za su nuna ƙwarewa wajen kamo waɗanda ke da hannu a kisan gillar.

Sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar a jiya alhamis, ta ruwaito Manjo Janar Abdussalam na ba da tabbacin cewar dakarun dake aikin farauto masu kisan gillar za su yi aiki da takwarorinsu dake ƙauyen Okuama domin sanin makama da kwarewa a aikin da za su gudanar a yankin.

KU KUMA KARANTA:Fyaɗe: An ba da belin Dani Alves, tsohon ɗan wasan Brazil kan dala miliyan 1.1

Kwamandan ya bayyana hakan ne a yau juma’a 21 ga watan Maris din da muke ciki lokacin da shugaban hukumar NDDC ta raya yankin Neja-Delta, Dr. Samuel Ogbuku ya kai masa ziyarar ta’aziya a hedikwatar rundunar haɗin gwiwar dake barikin sojoji ta birnin Fatakwal.

Da yake yabawa shugaban hukumar ta NDDC da tawagarsa game da ziyarar ta’aziyar, Manjo Janar Abdussalam yace aikin da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya dorawa rundunar shi ne na ƙwato makaman da masu kisan gillar suka sace da kuma tabbatar da an kama dukkanin masu hannu a aika-aikar.

Ya ƙara da cewar, dakarun za su ci gaba da aikinsu a yankin har sai sun cimma burinsu.

Leave a Reply