Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara rabon tallafin kayan abinci ga talakawa, da jami’an tsaron da ke Jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron buɗe-baki da jagororin tsaro a Gidan Gwamnatin jihar, inda ya yaba wa jami’an bisa ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da tsaro da walwalar Kanawa.
A cewar kakakinsa Sunusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan ya kuma jadadda kudirinsa na ci gaba da kare dukiya da rayukan al’ummar Kano a kokarin sauke nauyin da Allah Ya dora masa.
Abba ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu, bisa amincewa da rabon kayan abincin da ya ce za a fara a fadin jihar nan ba da jimawa ba .
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar
Kazalika, ya buƙaci jami’an tsaron da su dage wajen yi wa jihar da kasa baki daya addu’a a wannan watan na Ramadan, domin tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Waɗanda suka halarci buɗa-bakin dai sun haɗa da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar CP Muhammad Hussaini Gumel, Birgediya Janar M.A Sadiq na Rundunar Sojin Najeriya da ke Barikin Bukavu a Kano da sauransu.