Hukumar Kwastam shiyyar Sokoto da Zamfara, bisa bin umarnin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar na inganta samar da abinci, ta bayar da izinin sakin manyan motoci 15 da aka kama maƙare da hatsi ga masu su a ranar 12 ga Maris, 2024.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar a shiyyar, ta buƙaci ‘yan kasuwa da su gaggauta sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya, yana mai jaddada ƙudurin hukumar na yaki da ayyukan fasa-kwauri.
KU KUMA KARANTA: Mutane sun mutu a wurin sayen shinkafa mai rahusa ta Kwastam a Najeriya
Bugu da ƙari, Kwanturola Kamal ya sanar da kokarin hadin gwiwa tare da hukumar tattara bayanan sirri na Kwastam (CIU) da kuma kungiyar hadin gwiwa (JBPT) domin sanya ido kan yadda ake rarraba wadannan hatsi a kasuwannin cikin gida, tare da tabbatar da cewa ba za su samu hanyar fita daga ƙasar ta hanyoyin fasakwauri ba.
A nasa ɓangaren, sakataren ƙungiyar masu sayar da hatsi ta Sokoto Dahiru Ladan, ya nuna jin daɗinsa ga shugaba Tinubu bisa tausayawar da ya yi, ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ƙungiyar za ta tabbatar da cewa an sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya kaɗai.