Ƴan bindigar da suka sace ɗalibai 286 sun buƙaci kuɗin fansa naira biliyan ɗaya

Ƴan bindiga da suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Najeriya a makon da ya gabata, sun buƙaci a ba su Naira biliyan ɗaya, kwatankwacin dala 620,432 a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda kansilan yankin kuma mai magana da yawun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A ranar 7 ga watan Maris ne aka sace yara ƴan makarantar da ma wasu manyan ɗalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, a karon farko da aka yi garkuwa da mutane da dama irin haka tun shekara ta 2021.

Kansilan, Jubril Aminu, wanda kuma shi iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su suka zaɓa ya dinga magana a madadinsu, ya ce masu garkuwan sun ƙira shi ta wayar tarho ranar Talata.

“Sun buƙaci a biya su biya jimillar naira biliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa ga ɗaukacin ɗalibai da ma’aikatan makarantar,” in ji Aminu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace ‘yan makarantar Allo a Sakkwato

“Sun ba da wa’adin biyan kuɗin fansa cikin kwanaki 20, daga ranar da aka yi garkuwa da su, sun ce za su kashe dukkan ɗaliban da ma’aikata idan har ba a biya kuɗin fansar ba.”

Shi ma Idris Ibrahim, wani zaɓaɓɓen jami’i a karamar hukumar Kuriga, ya tabbatar da batun buƙatar kuɗin fansa da adadin kuɗin.

“E, masu garkuwa da mutane sun ƙira al’ummar ta lambar Jubril Aminu, suka kuma gabatar da buƙatar,” in ji shi.

Ibrahim ya shaida wa Reuters cewa, “Sun kira ne daga wata ɓoyayyiyar lamba amma hukumomi na aiki don gano lambar.”

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ɗaukar ƙwararan matakai domin ganin an sako ɗaliban.

Reuters ya ruwaito cewa Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, bai amsa saƙon da ta aika masa ta son jin ta bakinsa ba game da buƙatar masu garkuwa da mutane.

Haka shi ma mai magana da yawun Shugaba Tinubu bai amsa buƙatar son jin ta bakinsa ba.

Sai dai, Ministan yaɗa labaran kasar, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa, matsayar Tinubu kan sace-sacen da aka yi a Kuriga shi ne jami’an tsaro su tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan masu garkuwa da mutanen ba.

“Shugaban ƙasa ya ba da umarnin cewa dole ne jami’an tsaro cikin gaggawa su tabbatar da cewa an dawo da waɗannan yaran da duk waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya, sannan kuma su tabbatar ba a biya ko sisin kwabo domin kuɗin fansa ba.”

Gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta kafa dokar hana biyan kuɗin fansa inda ta ce za a ɗaure duk wanda aka samu ya biya kuɗin fansa don a sako wani nasa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *