Jama’a na nuna fargaba kan makomar Hisbah bayan murabus ɗin Sheikh Daurawa

0
129

Kamen masu aikata baɗala a wasu sassa na birni da kewayen Kano da damƙewa tare da gurfanar da matashiyar nan da ke kalaman batsa Murja Kunya a kotu, na daga cikin abubuwan da suka sabbaba wannan taƙaddama.

Masu fashin baƙi da al’ummar jihar Kano sun fara bayyana fargaba dangane da makomar hukumar Hizbah da ayyukan a arewacin Najeriya biyo bayan kalaman kushe ayyukan hukumar Hizbah da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar Alhamis, al’amarin da ya yi sanadiyyar Malam Aminu Ibrahim Daurawa sanar da ajiye shugabancin hukumar a ranar Jama’a.

Kamen masu aikata baɗala a wasu sassa na birni da kewayen Kano da damƙewa tare da gurfanar da matashiyar nan da ke kalaman batsa a kafar sadarwa ta zamani wato Murja Kunya, wadda sakin ta daga gidan gyaran hali kafi ranar zuwa kotu na daga cikin abubuwa da suka sabbaba tsamin dangantaka tsakanin gwamnan Kano da shugaban hukumar Hizbah ta jihar Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

A taronsa da wasu rukunin malamai na Kano a ranar Alhamis gwamnan na Kano anjiyo shi yana kushe ayyukan hukumar ta Hizbah, al’amarin daya sanya Malam Daurawa saka daga shugabancin hukumar.

Al’ummar jihar Kano dai na tsokaci akan wannan batu, inda yayin da wasu ke ganin ya kamata Malamai su rinƙa dogon nazari kafin su shiga cikin gwamnati saboda gudun abin da ka je ya zo, wasu kuwa cewa, bai kamata gwamnan ya fito fili ya kushe ayyukan hukumar Hizbar ba, tun da dai hukumace ta gwamnati kuma a ƙarƙashin kulawar sa take.

Gabanin kafa hukumar Hizbah a hukumance zamanin gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau a shekara ta 2003, wasu rukunin masu kishin musulinci ne suke gudanar da ayyukan Hizbah mai zaman kanta, lamarin da manazarta ke cewa siyasa ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ayyukan Hizbah a jihar dama wasu sassan arewacin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Da ɗumi-ɗumi: Aminu Daurawa ya sauka daga shugabancin Hisba a jihar Kano ( Bidiyo)

Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa shi ne babban daraktan hukumar na farko bayan kafuwarta a gwamnatance ya ce, “rawar da siyasa ta taka game da hukumar Hizbah shi ne ɗora ta akan doka ta yadda za ta iya kai ƙara za’a iya kai ƙararta, samar da kayan aiki ga hukumar da shugabannin da kuma ma’aikata da ware musu alawus da ba ta matsugunni, duk wannan ya inganta yadda ya kamata ayyukan Hizbar ya kasance”.

Sai dai yayin da ake samun rashin jituwa ta fuskar gudanar da aikace-aikacen hukumar Hizbah a tsakanin shugabannin siyasa da jagororin hukumar wasu Malamai a Kano na bayyana fargaba game da makomar ayyukan hukumar.

Malam Rabiu Musa Abdullahi na ɗaya daga cikin malaman musulunci a Kano na cewa, “hanyar da aka faro kuma a gwamnatance abin yake nunawa makomar Hizbah a Kano ‘yan Ƙato Da Gora ma sai sun fi ‘yan Hizbah kwarjini.”

Leave a Reply