Jami’an tsaron Najeriya sun kama biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance a wani samame da suka kai musu, a cewar jaridar the Financial Times, wadda ta ambato wasu majiyoyi da ke da masaniya game da batun ranar Laraba.
Shugabannin Binance ɗin sun je Najeriya ne sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar a ƙasar a makon jiya, sai dai nan-take ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro ya bayar da umarnin tsare su, in ji rahotanni.
Masu manjahar ta Binance ba su ce komai ba game da kama shugabannin nasu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A makon jiya gwamnatin Najeriya ta zargi Binance da taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin dala a ƙasar da kuma lalacewar darajar naira abin da ya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali.
Wata majiya daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya NCC ta tabbatarwa TRT Afrika Hausa cewa an bai wa kamfanoni na waya umarnin ɗaukar matakin, kuma har ma an fara aiki da shi, musamman ga masu amfani da waya.
KU KUMA KARANTA: CBN ya janye haramcin amfani da kuɗaɗen Kiripto
Ranar Talatar da ta wuce, gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wasu mutane da ba su sani ba “sun yi hada-hadar dala biliyan 26 ta manhajar Binance a Najeriya a cikin shekara ɗaya da ta wuce”.
Ya ƙara da cewa hakan yana barazana ga tattalin arziki da tsaron Najeriya.









