Fadar White House ta ce ba a gabatar wa Amurka da wani shirin Isra’ila na kare lafiyar fararen hula a Gaza ba idan har sojoji suka kutsa Rafah don fara kai hare-hare.
“Ba a gabatar mana da wani tsari ko ɗaya ba. Ba zan iya magana ga yawun Isra’ilawa ba ko kuma matakin da shirinsu ya kai ko kuma yadda hakan zai kasance ba,” in ji kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby a wani taron manema labarai.
Isra’ila na shirin faɗaɗa hare-hare ta kasa zuwa Rafah, birnin da ke kudancin Gaza da ke kan iyaka da Masar, kuma mahaifar Falasdinawa miliyan ɗaya da dubu 400 ne, a daidai lokacin da kasashen duniya ke gargadin illar da hakan zai haifar.
KU KUMA KARANTA: Falasɗinu ta buƙaci Isra’ila ta biya kuɗin sake gina Gaza
Kirby ya yi nuni da cewa, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ya ɗora wa janar-janar ɗinsa aikin samar da wani shiri.