Wata mata ta ɗauki nauyin kuɗin makarantar masu koyon aikin haɗa magunguna a New York

Makarantar koyon aikin likita a birnin New York za ta zama kyauta ga duk ɗalibai daga yanzu saboda gudummawar dala biliyan 1 daga wata tsohuwar farfesa, gwauruwar wani mai saka hannun jari na Berkshire Hathaway.

Lokacin da mijin Ruth Gottesman mai shekaru 96 ya mutu a cikin 2022, ya bar wani abu da ya ba matarsa mamaki, dala biliyan 1 a hannun jari na kamfanin hanayen jarin Berkshire Hathaway.

Gottesman ta gaya wa New York Times. cewa, umarnin mijinta kawai shi ne, “Ki yi duk abin da ki ga ya dace da shi,”

Da farko dai, Gottesman ta kasa yanke shawarar abin da za ti da wannan maƙudan kuɗaɗe, amma bayan ‘ya’yanta sun shawarce ta da kada ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta yanke shawara, sai ta yanke shawarar ba da gudummawar kuɗin gaba ɗaya ga Kwalejin Magunguna ta Albert Einstein da ke Bronx, da unguwa mafi talauci a birnin New York, in ji jaridar New York Times.

“Ina so in tallafa wa ɗalibai a Einstein domin su sami kuɗin koyarwa kyauta,” in ji ta.

Makarantar ta ce za a mayarwa dukkan ɗaliban da ke shekarar karatu ta huɗu a halin yanzu kuɗin da suka biya na karatunsu na bazara na 2024, kuma daga watan Agusta, duk ɗaliban makarantar na yanzu da waɗanda za a ɗauka gaba za su samu yin karatu kyauta.

KU KUMA KARANTA:Mahara sun kashe mutane 15 a wani Coci a Burkina Faso

Gottesman ta ba da sanarwar ga ɗaliban na yanzu da kanta a safiyar Litinin. Da zaran kalmar “karatu kwauta” ta fito daga bakinta, ɗaliban da ke ɗakin taron suka fashe da ihu, suna tafawa da tsalle daga kan kujerunsu, wasu na kuka, kamar yadda aka nuna a wani faifan bidiyo daga reshen asibitin makarantar, Montefiore Health System.

Gottesman, farfesa mai koyarwa a fannin likitan yara a Einstein, ta fara aikinta a kwaleji a 1968, a cewar sanarwar manema labarai na makarantar. Ta kasance shugabar kwamitin amintattu na makarantar, muƙamin da ta riƙe tun daga shekarar 2007 zuwa 2014.

Kuɗin koyarwa na shekara guda a makarantar ya haura dala 59,000, wanda hakan ya sa yawancin ɗaliban da suka kammala karatun su ke cin bashin fiye da dala 200,000, kafin su kallama makaranta kamar yadda binciken mujallar Times ya nuna.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *