Mahara sun kashe mutane 15 a wani Coci a Burkina Faso

0
77

Ƙasar Burkina Faso na daga cikin yankin kudu da hamadar sahara da ke fama da tashe-tashen hankula tun bayan yaƙin basasar Libya a shekara ta 2011.

Aƙalla fararen hula 15 ne aka kashe wasu biyu kuma suka jikkata a yayin wani harin ‘yan ta’adda da aka kai a wata cocin Katolika a lokacin da ake gudanar da taron sujada a ranar Lahadi a arewacin Burkina Faso, in ji wani babban jami’in cocin.

“Mun sanar da ku harin ta’addancin da aka kai kan mabiya ɗarikar cocin Katolika dake ƙauyen Essakane a yau 25 ga watan Fabrairu, a yayin da suka taru domin yin addu’o’i a ranar Lahadi,” in ji limamin cocin reshen Dori, Jean-Pierre Sawadogo a wata sanarwa da aka aika wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Ya ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai mutum 15 wasu 2 kuma suka jikkata.

Da yake ƙira kan samar da zaman lafiya da tsaro a Burkina Faso, Sawadogo ya yi tir da “waɗanda ke ci gaba da kashe-kashe a ƙasar.

Ƙauyen Essakane, inda aka kai harin, yana a yankin da ke da “iyakoki uku” a arewa maso gabashin ƙasar, a kusa da kan iyakokin ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.

Wannan dai shi ne hari na baya-baya a cikin jerin hare-haren da ake zargin ƙungiyoyin masu da’awar jihadi da ke fafutuka a yankin ne suka kaisu, inda wasu daga cikinsu suka kai hari kan majami’un Kiristoci yayin da wasu ke da hannu wajen sace malaman addinin Krista.

Burkina Faso dai na daga cikin yankin Sahel da ke fama da tashe tashen hankula tun bayan yaƙin basasar Libya a shekara ta 2011, sannan kuma a shekara ta 2012 mayaƙan IS suka karɓe arewacin Mali.

KU KUMA KARANTA:Al’ummar Nijar na maraba da matakin ECOWAS na janye musu takunkumi

Rikicin masu jihadin ya bazu zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar tun daga shekarar 2015.

A lokacin da Kyaftin Ibrahim Traore ya karɓe mulki a shekarar 2022, wannan ne ƙaro na biyu da aka yi juyin mulki a ƙasar ƙasa da shekara guda, duka biyun taƙaddama akan gazawar gwamnati wajen murƙushe masu jihadi ne suka haddasa su.

Kimanin mutane 20,000 ne aka kashe a Burkina Faso a wannan tashin hankalin, yayin da sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu.

Leave a Reply