Bayan ya yi shekaru 37 a Kurkuku, an gano ba shi ne ya yi kisan ba

0
101

Hukuma za ta biya wani mutumin Florida diyyar dala Miliyan 14 saboda ɗaure shi shekaru 37 bisa kisan da bai shi ne ya aikata ba.

Robert Duboise ya shafe shekaru 37 a gidan yarin Florida saboda laifin fyaɗe da kisan kai a 1983 da bai aikata ba. Yanzu jihar Florida za ta biya shi dala miliyan 14 a matsayin diyya na tsawon shekarun da yake ɗaure.

An dai yanke wa Duboise wadda ke shekaru 18 a lokacin da laifin ya auku hukuncin kisa da farko saboda kashe Barbara Grams mai shekaru 19. Ko da yake daga baya an rage hukuncin ɗaurin sa zuwa rai da rai a gidan yari, sai dai a shekarar 2018 tare da taimakon ƙungiyar da ke kare waɗanda ake kyautata zaton ba su aikata laifin da aka ɗaure su a kai ba, masu shigar da ƙarar suka amince su sake waiwayar ƙarar.

Gwajin DNA da a lokacin babu shi a shekarar 1980, ya nuna alamun wasu mutane biyu ne ke da hannu a kisan, wanda ya kai ga sakin Duboise daga kurkuku a 2020. Ba da daɗewa ba, Duboise ya kai ƙarar birnin Tampa da ke Jihar Florida, da jami’an ‘yan sanda waɗanda suka binciki lamarin da kuma likitan haƙora wanda ya shaida cewa haƙoransa sun yi daidai da alamar cizon wadda aka kashen.

KU KUMA KARANTA:Hisbah ta cafke Ramlat Princess bayan ta tallata kanta akan maɗigo

An dai daidaita ƙarar ne a ranar 11 ga watan Janairu amma Majalisar birnin Tampa ta kaɗa ƙuri’ar amincewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata tare da ba Duboise dala miliyan 14 a hukumance, wanda ya kai shekaru 59 a yanzu. Mambobin Majalisar sun ce kuɗin shi ne mafi ƙarancin abin da birnin zai iya yi masa.

“Wannan babban kuskure ne,” in ji dan Majalisa Luis Viera. “Ina fata da kuma addu’ar cewa zai dan sami sa’ida daga wannan biyan diyyar.”

DuBoise da kamfanin lauyoyinsa za su samu dala miliyan 9 a bana, dala miliyan 3 a shekara mai zuwa da dala miliyan 2 a shekarar 2026, a cewar takardun.

An dai yi lalata ne da Barbara inda aka kuma yi mata duka aka kashe ta a watan Agusta 1983 yayin da ta ke komowa gida bayan ta tashi daga shagon cin abinci da take aiki a Tampa.

Leave a Reply