Najeriya ta kai wasan ƙarshe na gasar AFCON

0
202

Najeriya ta kai wasan ƙarshe na Gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON bayan doke Afrika ta Kudu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

A bugun faneratin da aka yi bayan shafe mintuna 120 ana barje gumi, Najeriya ta sami nasarar cin kwallaye 4 yayin da Afrika ta Kudu ta ci kwallaye 2.

Wannan ne karon farko cikin shekaru 10 da tawagar ta Super Eagles ta tsallaka wasan ƙarshe na Gasar AFCON.

A daidai ƙarfe 6:00 na yamma agogon Najeriya aka soma fafatawar, inda aka tafi aka dawo daga hutun rabin lokaci babu tawagar da ta samu nasarar zura ƙwallo a raga duk da hare-haren da aka riƙa kai wa juna.

Najeriya ce ta soma zura wa Afrika ta Kudu kwallo ɗaya a minti 67 da take wasan.

Mai tasaron baya kuma kyaftin ɗin Najeriya William Ekong ne ya ci ƙwallon a bugan fanareti.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta tsallaka zuwa wasa na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afirka

Victor Osimhen ne ya samo fanaretin bayan da aka taɗie shi a da’irar yadi 18.

Sai dai murna ta koma ciki, inda Afirka da Kudu ta rama ƙwallon da aka zura mata a minti na 90.

Ɗan wasan Afirka ta Kudu T. Mokoena ne ya zura ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Hakan ta faru ne bayan an buge ɗan wasan Afirka ta Kudu a gaban mai tsaron ragar Najeriya.

Haka aka rarrafa aka shiga zangon ƙarin lokaci a wasan kuma aka karkare ba tare da wata tawaga ta yi galaba a kan abokiyar karawarta.

Da wannan nasara da Super Eagles ta samu, za ta buga wasan ƙarshe da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin mai masaukin baƙi Ivory Coast da DR Congo.

Leave a Reply