‘Yan bindiga sun kashe basarake, sun yi tafi da matarsa a Kwara

0
123

Daga Maryam umar Abdullahi

Wasu mutane ɗauke da makamai sun harbe wani basaraken gargajiya, tare da yin garkuwa da matarsa da kuma wani mutum guda a yankin arewa maso tsakiyan Najeriya, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Maharan dai sun kai farmaki ne a fadar Segun Aremu, janar ɗin soja mai ritaya kuma basarake mai suna Olukoro na Koro a daren ranar Alhamis.

Ba a dai bayyana ko su waye ‘yan bindigar ba ko kuma masu neman kuɗin fansa ne ko kuma a’a.

KU KUMA KARANTA:Masu gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano

Wannan sabon kisa da sace mutane ya zo ne kwanaki bayan masu fafutuka sun buƙaci a kafa dokar ta ɓaci domin shawo kan lamarin.

Wasu ƙungiyoyin farar hula 50 ne ke son shugaba Bola Tinubu ya yi wannan iƙirarin, inda aka ce sama da mutane 1,800 aka sace tun bayan hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake yin Allah wadai da kisan da aka yi wa Olukoro na Koro a jihar Kwara, a matsayin “rashin hankali, mai ban tsoro, kuma abin ƙyama”, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya sha alwashin kama waɗanda suka aikata wannan laifin. ‘Yan sanda kuma sun ce ana farautar mutanen.

Leave a Reply