Gamayyar ƙungiyoyin farar hula ta Najeriya ta ɗorawa hukumomi alhakin rashin tsaro

0
129

Daga Maryam Umar Abdullahi

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula sama da 40 sun kai ƙarar shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda suka yi ƙira gare shi da ya magance matsalar rashin tsaro da ta ƙara ƙamari tun bayan hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.

Koken ya biyo bayan wasu sace-sacen da aka yi a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin ƙasar.

A wani rahoto da gamayyar ƙungiyoyin farar hula suka fitar a wannan makon, an bayyana cewa, an kashe aƙalla mutane 2,400 tare da yin garkuwa da wasu kusan 1,900 tun watan Mayun bara lokacin da Tinubu ya karɓi mulki.

Ƙungiyar ta ce ta damu matuƙa da taɓarɓarewar tsaro a faɗin Najeriya inda ta yi ƙira ga hukumomi da su ɗauki matakan da suka dace don magance matsalar.

Auwal Rafsanjani, babban daraktan cibiyar kare haƙƙin fararen hula, wanda ya yi magana a madadin ƙungiyar ya ce, “Rashin tsaro ya mamaye ƙasarmu, ‘yan ta’adda sun mamaye ƙasarmu, ‘yan fashi da makami, ‘yan bangar siyasa, ana kashe ‘yan Najeriya kamar tururuwa, kowace ranar da kuka farka, sai dai a ji kisa bayan kisa, ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba.”

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai munanan hare-hare a ƙasar ciki har da Abuja.

A birnin Abuja, wasu gungun masu ɗauke da makamai sun kai hare-hare na garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a makonnin da suka gabata. An kashe mutane biyu daga iyalai daban-daban a matsayin gargaɗi ga waɗanda ba su biya ba.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC, ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta naɗa don warware rikicin Mangu

A jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin ƙasar, a kwanakin baya wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban makaranta shida da malamai uku. Hari ila yau, a ranar, wasu ‘yan bindiga suka kuma kai hari a wasu ƙauyukan jihar tare da kashe wasu sarakunan gargajiya guda biyu.

Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren sannan ya umarci jami’an tsaro da su kamo waɗanda suka kai harin.

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin tsaro Chidi Omeje ya ce gazawar gwamnati ce ta haifar da matsalar da ake fama da ita.

Tushen duk waɗannan abubuwa shi ne rashin shugabanci, rashin shugabanci ke haifar da talauci, takaici, da fushin jama’a, in ji shi. “Duba, akwai alaƙa tsakanin talauci, rashin shugabanci da kuma yaɗuwar aikata laifuka.”

A bara, Tinubu ya sha alwashin magance matsalolin tsaro a Najeriya idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Bayan hawansa mulki, Tinubu ya yi wa wasu hafsoshi ritaya tare da naɗa sabbi.

Leave a Reply