Kotu ta ba da belin Ɗanbilki Kwamanda

0
169

Daga Ibraheem El-Tafseer

A jihar Kano, an saki fitattaccen ɗan siyasar nan Ɗanbilki Kwamanda bayan da wata kotun majistire ta bayar da belinsa.

Lauyan Ɗanbilki ya shaida wa BBC cewa an sake shi ne bayan ya cika sharuɗɗan belin da kotun ta gindaya masa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta aike da Ɗanbilki Kwamanda gidan gyaran hali a Kano

Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda ne bisa zargin yin wasu kalamai da kotun ta ce ka iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun Kano.

Leave a Reply