Abubuwan al’ajabi da ke tattare da dabbar ‘Batoyi’ (Hotuna)

0
158

Wannan dabbar ita ake ƙira da Hausa da ‘Batoyi’ wasu kuma su na ƙiranta da ‘Ɗankunya.’

Ana kuma samun wannan dabbar a nahiyar Asiya da kuma yankin kudu da hamadar sahara a Afirka.

An yi imanin cewar, su ne mafi yawan fataucin dabbobi masu shayarwa a duniya.

Ana farautar dubun-dubatar Ɗankunya kowace shekara, ana kuma kashe su saboda amfaninsu na magungunan gargajiya na da ƙasar Sin ke yi da kuma cin namansu. Kana ana amfani da fatar wajen ƙera rigunan silke na harsashin bindiga (bulletproof).

Akwai nau’ikan Ɗankunya har guda takwas. Ana samun huɗu a nahiyar Asiya; Sin, Sunda, Indiya, da Philippine. Hukumar IUCN ta lissafta na ƙasar Philippine a matsayin mafi hatsarin gaske.

Dukkan nau’ikan takwas suna fuskantar raguwa saboda yawan haramtacciyar farautasu da ake yi domin fatauci.

A shekara ta 2016, ƙasashe 186 da ke cikin yarjejeniyar cinikayyar ƙasa da ƙasa na namun daji (CITES), sun yi yarjejeniyar da ke daidaita cinikin namun daji na ƙasa da ƙasa, inda suka kaɗa ƙuri’ar haramta cinikayyar dabbar.

Ɗankunya, sun kasance masu kaɗaita al’amuransu da rana, wadda galibi sun fi yin walwala da daddare. Yawancin su na rayuwa ne a doron a ƙasa, amma wasu, kamar Pangolin black-bellied su na hawan bishiyoyi.

Sun kasance da ɗan girma da kuma tsayi fiye da ƙafa huɗu. Su na rufe da kariya, kamar dai farcen ɗan adam, wadda ake masu laƙabi da “Scaly Anteater.”

Lokacin da aka yi matsa masu, suna mirginawa kamar ƙwallo, kuma suna iya sakin wani ruwa mai wari daga gindin wutsiyarsu a matsayin hanyar kariya.

Ɗankunya suna da dogon hanci har ma da harsuna masu tsayi, waɗanda suke amfani da su don ƙwanƙwasa tururuwa da suke tonowa daga tudu da faratansu masu ƙarfi. Bugu da ƙari, suna iya rufe hanci da kunnuwansu don hana tururuwa ko ƙwari shiga a lokacin da suke ci.

Ko da yake sun fi kamanceceniya da kuma ɗabi’a irin ta dabbar anteaters da armadillos, Ɗankunya sun fi kusanci da Maguna, da kuma Karnuka.

Ana haihuwar jarirai da kariya (scale) mai laushi wadda bayan kwana biyu ya ke yin tauri, inda suke hawan wutsiyar uwayensu har sai an yaye su a kusan watanni uku. Yayin da kuma suke isa shekarun girma (balaga) a shekara biyu.

Girmansu ya na kai inci 45, tsayi kuma 4.5, nauyi kuma 4 zuwa fam 72.

Ana amfani da gurzin jikinsu domin yin ababe da dama kamar su; Farcen hannu, gashi, da ƙawo. Har ila yau, gurzin jikin Ɗankunya kamar ƙahon Karkanda ne, ba su da tabbataccen amfani a matsayin magani a hukumance, amma duk da haka ana amfani da su a cikin magungunan gargajiya na ƙasar Sin da Vietnam don taimakawa rage cututtuka irin su ciwon huhu da sauran su.

KU KUMA KARANTA: Abubuwan da ba ku ji ba game da ƙasar Mozambik (Hotuna)

Haka nan, idan aka busar ya zama hoda, za a iya juya shi zuwa ƙwayoyin magani na amfani.

Shekaru da dama, nau’in Ɗankunya na yankin Asiya su ne farkon abin da masu farauta da masu fatauci su ke kai wa hari.

Amma yanzu da adadinsu ya ragu, masu fasa-ƙauri na ƙara karkata zuwa ga na nahiyar Afirka.

An tattara cewa, a cikin watan Afrilu na 2019, Singapore ta kama jigilar tan 14.2 da kuma jigilar tan 14 na ma’aunin Ɗankunya, daga ƙiyasin 72,000 wadda sun fito ne daga Najeriya.

Leave a Reply