Da Ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Fintiri na Adamawa

0
112

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Kotun ƙolin ta kori ƙarar da ‘yar takarar kujerar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar APC a babban zaɓen 2023, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, da ta shigar tana mai ƙalubalantar ayyana gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, a matsayin gwamnan jihar Adamawa.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a John Okoro, ta tabbatar da cewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shi ne halastaccen gwamna a jihar Adamawa.

Haka kuma Mai shari’a John Okoro ya bayyana cewa matakin da Kwamishinan hukumar Zaɓe na jihar (REC), Hudu Ari, ya ɗauka, wani aiki ne na rashin gaskiya da kuma aikata laifi.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta yaba wa hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen gwamnan Kano

Mai shari’a Okoro ya ci gaba da cewa, jami’i Mai sanar da sakamakon zaɓe ya kamata ya bayyana sakamakon zaɓe, domin a kaucewa hargitsi da ruɗani.

Ya bayyana cewa dokar zaɓe ta ba da alhakin wanda zai bayyana sakamakon zaɓe, kuma wannan iko ya rataya ne kawai ga jami’in da hukumar zaɓe INEC ta aiko Mai sanar da sakamakon zaɓe.

Leave a Reply